Fani Kayode, Shehu Sani sun ziyarci gwamnan da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ana rade-radin za su bi sahu
- Yayin da ake tsaka da hada-hadar siyasa a Najeriya gabanin zaben 2023, Fani-Kayode ya ziyarci Gwamna Matawalle na jihar Zamfara
- Jigon na PDP ya ce ya kuma gana da Sanata Shehu Sani a masaukin gwamnan jihar Zamfara da ke Abuja
- Ziyarar da mutanen biyu suka kaiwa gwamnan na Zamfara wanda bai dade da barin PDP zuwa APC ba na iya haifar da sabbin rade-radin sauya sheka
FCT, Abuja - Femi Fani-Kayode, jigo a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ya ziyarci gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a Abuja.
Jigon na PDP ya bayyana hakan ne ta wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuli.
Legit.ng ta lura cewa hotunan da tsohon ministan sufurin jirgin ya wallafa sun kuma nuna cewa Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna, shima yana tare da Gwamna Matawalle.
Sakon jigon na PDP ya zo kamar haka:
“Na samu damar raya daren jiya a Gidan Gwamnan jihar Zamfara da ke Abuja tare da abokina kuma ɗan'uwana Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara.
"Mun tattauna kan siyasa da al'amuran kasa har zuwa wayewar gari.
"Abin farin ciki ne ganin tsohon abokina Sanata Shehu Sani, mutum mai kwarjini da kima sosai, mai karfi a siyasa kuma mai sharhi kan lamuran siyasa a can."
Fani-Kayode ya kuma yabi Matawalle, inda ya bayyana shi a matsayin jagora nagari.
Kalmominsa:
"A nasa bangaren Matawalle na daya daga cikin hazikan shugabannin da suka fito fili a siyasar Najeriya kuma, a matsayinsa na aboki, ya kasance mai tsayin daka kamar tauraron arewa.
"Baya ga kasancewarsa daya daga cikin manyan masu gina kasar nan ya kuma kasance mutum da ke da karfin gwiwa wajen daukar matakan da suka dace, shi ne kuma Matawallen Maradun yayin da ni na kasance Sadaukin Shinkafi. Shi da ni daya ne kuma ina alfahari da nasarorin da ya samu a jihar Zamfara!
"Allah ya ci gaba da jagora da kuma kasance tare da shi da mutanen kirki na Zamfara."
Me yasa ziyarar da Fani-Kadoye ya kai wa Matawalle ya zama abun zargi?
A cikin ‘yan watannin da suka gabata, Fani-Kayode ya zagaya jihohi daban-daban a fadin kasar, inda ya kwashe kwanaki tare da gwamnonin jam’iyyar PDP da All Progressives Congress (APC).
Wannan ya haifar da jita-jitar cewa yana tunanin sauya sheka zuwa APC ne. Sai dai kuma, daga baya ya warware jita-jitar, yana mai cewa har gobe shi jigon PDP ne.
Duk da haka, ziyarar da ya kaiwa Gwamna Matawalle wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC na iya haifar da sabbin rade-radin sauya sheka.
Shin Shehu Sani na son komawa APC ne?
Gabannin zaben 2019, Sanata Sani ya bar APC zuwa jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP).
Sai dai kuma, bai samu komawa majalisar dattijai ta tara a karkashin jam'iyyar PRP ba.
Kwanan nan, ya sanar da ficewarsa daga PRP amma bai nuna wace jam’iyya zai shiga ba a nan gaba. Ziyarar tasa ga Gwamna Matawalle na iya kuma haifar da jita-jita game da yiwuwar komawarsa APC.
Sauya Sheka: PDP bata da hankali da take wa Matawalle barazana, Fani-Kayode
A baya, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, ya zagi jam'iyyarsa kan barazanar da take na maka Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a gaban kotu kan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC.
Fani-Kayode a jerin wallafar da ya dinga a shafinsa na Twitter, ya soki barazanar da ake wa Matawalle inda ya shawarci jam'iyyarsa da ta dage wurin janyo hankali, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng