Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu
- Gwamnatin Zamfara ta yi gargadin karshe ga mutanen da ke fataucin mutane a jihar
- Gwamnatin a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, ta yi wa mazauna yankin alkawarin cewa daga yanzu za a yi hukunci mai tsanani kan laifin
- Bugu da ƙari, gwamnan, Bello Matawalle, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da fifikon buƙatu da jin daɗin mata da yara
Gusau, Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sake nanata matsayinta na kin lamuntan fataucin mutane don haka ta yi kira da a dauki tsatsauran hukunci kan laifi.
Gwamna Matawalle ne ya yi wannan kiran a yayin wani biki da aka gudanar a gidan Babban Kwamishinan Burtaniya da ke Abuja a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai matukar bukatar yanke hukunci mai tsanani ga mutanen da ke cikin tashin hankali da ya danganci jinsi da kuma masu taimaka musu, Channels TV ta ruwaito.
Gwamnan wanda ya sami wakilcin babban sakataren ma’aikatar kula da ayyukan jin kai na jihar, Bala Umar Tsafe, a wani taron mai taken Ranar yaki da Fataucin Mutane na duniya, ya ce taron zai sa a gano masu aikata laifukan.
Ya kara da cewa taron zai kuma nuna mahimmancin sauraro da koyon darasi daga waɗanda suka tsira daga lamarin kuma ta haka ne za a samar da kyakkyawar hanyar magance ta.
Matawalle ya sha alwashin cewa gwamnatinsa, tare da sanin karuwar laifuka a kan jinsin mata, za ta kafa kwamiti karkashin jagorancin uwargidan gwamnan Zamfara don tabbatar da manufofi da shirye-shirye ga mata da yara, ta haka za a daidaita da kuma saita masu tunaninsu.
A wani labari na daban, Ministan tsaro Bashir Magashi ya bayyana wasu dalilai da ke haifar da matsalar tsaro a Najeriya.
Magashi ya ce rashin 'yan siyasa da sarakunan gargajiya a matakin kananan hukumomi na haifar da wani gurbi wanda masu aikata laifi ke amfani da shi.
Ministan ya kuma yi zargin cewa masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a yankin arewa sun yi sulhu.
Asali: Legit.ng