Sanatan APC Ya Kwance Wa Tinubu Zani a Kasuwa, Ya Ce Wasu Yan Tsiraru ke Amfana da Gwamnatinsa
- Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce yana cikin waɗanda suka taka rawa wajen gazawar siyasar Najeriya
- Ya bayyana cewa gwamnati mai ci tana kokarin jare muradan wasu tsirarun mutane ne kawai, ba al'umma gaba daya ba
- Ndume ya yi gargaɗi kan ƙaruwar rikicin siyasa, inda ya ce ya kamata a ɗora wa masu ɗaukar nauyin tashin hankali alhaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya amince cewa yana cikin waɗanda suka taka rawa wajen gazawar siyasar Najeriya.
Sanata Ndume ya kuma soki gwamnati mai ci karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa gwamnati ce ta wasu mutane, da wasu mutane, domin wasu mutane.

Source: Facebook
Da yake magana a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, sanatan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda masu riƙe da muƙaman gwamnati ke tara dukiya, yana mai cewa da yawa daga cikinsu masu haɗama ne.
Ndume ya ce siyasa ta gurbace
Ndume ya kuma nuna damuwarsa kan yadda tashin hankalin siyasa ke ƙaruwa a ƙasar, inda ya ce ya kamata a hukunta duk wanda aka samu da ɗaukar nauyin irin waɗannan ayyuka.
Ya ce
"Ina cikin waɗanda suka jawo gazawar, ba zan iya musanta hakan ba. Ba zan ce ni ne na fi kowa gaskiya ba amma da na san cewa siyasa za ta zama haka, da ban shiga cikinta ba.
"Za ka iya kwatanta siyasa da cutar AIDS. Da zarar ka kamu da ita, ba za ka ce ba ka da ita ba. Bari na fada maka, wasa ne mai haɗari, musamman a Najeriya, ba za ka iya warkewa daga gare ta ba.
Sanatan na jihar Borno ya kuma soki gwamnati mai ci, yana mai cewa wasu tsiraru ne ke amfana da ita.
“Gaskiya ne, gwamnatin mai ci gwamnati ce ta wasu mutane, da wasu mutane, domin wasu mutane amma ba ta kowa ba ce, ga gwamnati ta kowa ce, da ba a samun waɗannan koke-koke da makamantansu ba.

Kara karanta wannan
Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu
"Ba wannan gwamnatin ce ta fara hakan ba, gwamnatin da ta gabata ce ta fara. Ya zama al’ada cewa dole ne mutum ya kasance cikin waɗanda ke da iko, ko a cikin waɗannan mutanen ma, akwai wasu tsirarun da ke tafiyar da gwamnati.”
- Sanata Ali Ndume.
Ndume ya yi magana kan tashin hankali
Da yake magana kan amfani da tashin hankali a matsayin hanyar fafatawa a siyasa, ya ce sun dauki matakin dakile lamarin a bangaren Majalisa.
Ya nuna farin cikinsa kan yadda kowa ya nuna damuwa kan abubuwan da ke faruwa a siyasar Najeriya, yana mai cewa kudirin da aka gabatar a Majalisa ba shi da alaka da siyasa.
"Wannan na daga cikin ƙudurorin da ba su da alaƙa da siyasa, domin matsalar tamkar wuta ce, idan ta kama, ba ka san lokacin da za ta tsaya ba, kuma za ka iya fuskantar matsala wajen kashe ta," in ji shi.
Ndume ya yi nadamar shiga siyasa
Kun ji cewa Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana nadamarsa kan shiga siyasar Najeriya.
Sanatan ya kuma yi gargaɗin cewa rashin haƙuri da juna a siyasa, rashin aikin yi da rashin hukunta masu laifi na iya kawo cikas ga sahihancin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
