Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Doyin Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce da kyar idan akwai wani banbanci tsakanin jam'iyya mai mulki ta APC da ta PDP.
Tuni aka shirya hukumomin tsaro a babban birnin tarayya domin dawowar shugaban kasa wanda ake sa ran zai iso da karfe 5 na yammacin yau, 13 ga watan Agusta.
Dan takarar gwamnan jihar Yobe na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Ambasada Umaru Damagum, yace bai da masaniya a kan karar da aka ce ya shigar don tsige Mala Buni.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar a kan jam'iyyar mai mulki da shugabanta, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, ta shigar da kara na neman tsige Mai Mala Buni daga mukaminsa na gwamnan Yobe.
Alhaji Muhammad Sani Idris, kwamishinan labarai na jihar Neja ya bayyana cewa abokan hamayya ne suka yo haya 'yan bindigan Zamfara domin su yi garkuwa da shi.
Rundunar sojin Najeriya a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta ta amsawa Misis Oluwaseun Sakaba, matar marigayi Kanar Ibrahim Sakaba, ta ce bata kashe mijinta ba.
Matar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Shehu Usman Aliyu Shagari ta rasu bayan fama da cutar korona. Hajiya Hadiza Shehu Shagari ta rasu ne a ɗaren Alhamis.
Aruwan ya ce wadanda suka tsere sun hada da wadanda aka yi garkuwa da su daga Dumbin Rauga a karamar hukumar Zariya da kuma kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Aisha Musa
Samu kari