Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta garzaya kotu don korar Mai Mala Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe
  • An ce Buni, wanda shine shugaban kwamitin riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya sabawa kundin tsarin mulki saboda rike mukaman zartarwa guda biyu lokaci guda
  • Jam'iyyar adawa na son kotu ta ayyana dan takararta na gwamna a 2019 a jihar Yobe a matsayin wanda ya lashe zaben

FCT, Abuja - An gurfanar da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a kotu kan nadinsa a matsayin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, ta shigar da kara na neman a cire Buni daga mukaminsa na gwamnan Yobe.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: PDP ta bukaci a gaggauta tsige Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe

Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe
Jam'iyyar PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe Hoto: APC
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa a cikin karar da aka shigar a ranar 12 ga watan Agusta, PDP ta gabatar da cewa Buni ya sabawa sashe na 183 na kundin tsarin mulki lokacin da ya yarda yayi aiki a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na APC duk da cewa yana rike da mukamin gwamna.

Dan takarar gwamnan Yobe na PDP a zaben 2019, Umar Damagum, da abokin takararsa, Baba Aji, sune suka shigar da kara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karar da lauyansu, Emeka Etiaba ya shigar, PDP ta dage cewa Buni ya tashi daga gwamna tun daga lokacin da ya yarda ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin riko na APC.

PDP ta nemi kotu ta ayyana dan takararta a matsayin gwamnan jihar Yobe

Don haka, masu karar sun roki kotun da ta umarci babban alkalin Yobe ko wani babban mutum kusa da babban alkalin da ya gaggauta rantsar da Damagum da Aji a matsayin gwamna da mataimakin gwamnan jihar, kasancewar sune suka zo na biyu a zaben gwamna a jihar a 2019.

Kara karanta wannan

Ba ma bukatarka kuma: Yan majalisa na PDP sun nemi Secondus ya yi murabus a matsayin shugaban jam’iyyar

A wani labarin, biyo bayan kalaman jama'a kan zaman da jigogin APC suka yi idan akayi kalaman suka ga shugaba Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, ya kare kansa.

Bindow a jawabin da ya saki ta hannun mai magana da yawunsa, Sadiq Abdullateef, Bindow yace ya halarci taron ne matsayin mai sulhu tsakanin bangarorim jigogin APC a Yola ta kudu biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng