Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

  • Ana sa ran dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari gida Najeriya a yau, Juma’a, 13 ga watan Agusta
  • Tuni aka shirya jami’an tsaro a babbar birnin tarayyar domin isowar Shugaban kasar da karfe 5:00 na yamma
  • Buhari dai ya je Landan ne domin halartan wani taro na ilimi inda daga nan ya tsaya ganin likitansa

Landan - Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya da karfe 5:00 na yammacin yau Juma’a, 13 ga watan Agusta, bayan kimanin makonni biyu a kasar Ingila.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa tuni aka shirya hukumomin tsaro a babban birnin tarayya domin dawowar shugaban.

Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau
Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau Juma'a Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shugaban kasar dai ya yi tafiyar ne don halartar taron Ilimi na Duniya kafin ya tsaya domin duba lafiyarsa.

Shugaba Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara har gidansa a Landan

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara har gidansa a Landan

A gefe guda, mun ji cewa mai girma shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara da kansa zuwa gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Landan, kasar Ingila.

Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad ya fitar da hotunan wannan gana wa da aka yi tsakanin manyan kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari, Muhammadu Buhari ya ziyarci tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021.

PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

A baya mun kawo cewa, Jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Shehu Shagari

PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.

PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel