Ana tsaka da Kamfen a Najeriya, Tinubu Ya Gamu da Gagarumar Koma Baya a Arewa
- Emmanuel Zopmal ya yi watsi da matakin wasu shugabannin Middle Belt na marawa Shugaba Bola Tinubu baya domin ya sake zabensa
- Shugaban matasan ya ce ba a tuntubi matasa, mata, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kafin sanar da goyon bayan Tinubu ba
- Zopmal ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, inda ya ce za su wayar da kan al'ummar yankin domin su zaɓe su a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Shugaban matasan ƙungiyar Middle Belt Forum (MBF), Emmanuel Zopmal, ya yi watsi da matakin wasu shugabannin yankin na marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.
Maimakon haka, Zopmal ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Zopmal ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake ganawa da manema labarai a Jos, babban birnin jihar Plateau.
A yayin taron, ya gabatar da matsayar shugabannin matasan Middle Belt kan makomar siyasar yankin gabanin zaɓen 2027.
Zopmal ya yi watsi da goyon bayan Tinubu
Shugaban matasan ya ce matakin da wasu shugabannin suka ɗauka bai wakilci muradin al'ummar Middle Belt ba.
Ya zargi waɗanda suka shirya ziyarar zuwa wurin Shugaba Tinubu da rashin tuntubar muhimman masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin al'umma, sarakunan gargajiya, matasa da mata.
A cewarsa, ba a yi cikakkiyar shawara da mutanen da ke fuskantar matsalolin tsaro a yankin ba kafin bayyana goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Zopmal ya ce:
"Ba a tuntubi al'ummomin Middle Belt, dattawa, sarakunan gargajiya, matasa da mata waɗanda ke fuskantar munanan abubuwan da ke faruwa a yankunansu ba kafin sanar da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027."
Ya bayyana matakin a matsayin wanda bai yi la'akari da matsalolin tsaro da tattalin arziki da al'ummar yankin da ƙasar baki ɗaya ke fuskanta ba.
Sannan ya lissafa rashin tsaro, tsadar rayuwa, hauhawar farashi, yawan bashi da talauci a matsayin manyan matsalolin da ya kamata a fara magancewa.

Source: Original
Ya soki shugabancin Middle Belt Forum
Zopmal ya kuma yi tambaya kan tsarin shugabanci da gudanar da ayyukan ƙungiyar Middle Belt Forum.
Ya yi zargin cewa ƙungiyar ta shafe shekaru takwas ba tare da babban taron wakilai, zaɓen shugabanni, bin kundin tsarin mulki da kuma tsarin bayar da bayanan yadda ake tafiyar da ayyukanta ba.
Ya bukaci ƙungiyar ta koma tafiyar da al'amuranta bisa tsarin dimokuraɗiyya tare da samar da ingantacciyar alkibla ga fafutukar yankin.
Haka kuma, ya soki tsohon shugaban ƙungiyar, Dakta Pogu Bitrus, bisa abin da ya kira rashin gudanar da shawarwari da kowa a cikin ayyukan ƙungiyar.
Ya ce babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon magana a madadin daukacin al'ummar Middle Belt ba tare da samun yardarsu da shigar dukkanin sassan ƙungiyar ba.

Kara karanta wannan
"Yadda Pater Obi da Kwankwaso za su kifar da Tinubu a zaben 2027 da taimakon Allah"
Ziyarar shugabannin yankin wurin Tinubu
Da yake magana kan ziyarar da wasu shugabannin Middle Belt suka kai wa Shugaba Tinubu, wadda tsohon babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Theophilus Danjuma mai ritaya, ya halarta, Zopmal ya yi zargin cewa muradun siyasar wasu mutane ne suka rinjayi ziyarar.
Ya nuna damuwa kan yadda za a iya danganta sakamakon ganawar da matsayin Janar Danjuma ba tare da samun cikakken amincewar al'ummar yankin ba.
Ya kuma ce Middle Belt Forum ba ƙungiyar siyasa ba ce, don haka bai fahimci dalilin da ya sa ba a gayyaci wakilan jam'iyyun adawa daga yankin zuwa ganawar ba.
'Babu matsala tsakanin Tinubu da Makinde'
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Olugbon na Orile-Igbon, Oba Francis Alao, ya ce babu wani saɓani tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.
Basaraken ya kuma bayyana cewa za a warware duk wata saɓani da ke tsakaninsu idan ma akwai kafin zaɓen 2027.
Sarkin ya kuma ce yankin Kudu maso Yamma ya kamata ya ci gaba da riƙe shugabancin ƙasa har zuwa 2031.
Asali: Legit.ng

