Da dumi-duminsa: Mutane 5 sun mutu a wani sabon harin da aka kai kan ofishin ‘yan sanda

Da dumi-duminsa: Mutane 5 sun mutu a wani sabon harin da aka kai kan ofishin ‘yan sanda

  • 'Yan bindiga sun sake kai farmaki ofishin 'yan sanda na Izombe dake karamar hukumar Oguta a jihar Imo
  • Harin wanda ya afku a safiyar ranar Asabar ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar
  • Daga cikin wadanda suka mutu akwai jami'an 'yan sanda biyu sai kuma uku daga cikin maharan

Mutane biyar sun mutu a safiyar ranar Asabar, 14 ga watan Agusta, lokacin da wasu yan daba suka mamaye hedikwatar yan sandan Izombe dake karamar hukumar Oguta a jihar Imo, jaridar Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa yayin da aka harbe 'yan sanda biyu da ke bakin aiki, uku daga cikin maharan ma sun rasa rayukansu.

Da dumi-duminsa: Mutane 5 sun mutu a wani sabon harin da aka kai kan ofishin ‘yan sanda
An yi artabu tsakanin maharan da 'yan sanda Hoto Daily Trust
Asali: UGC

Maharan wadanda suka yi shirin tayar da bam a ofishin sun yi musayar wuta da 'yan sandan wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamnatin Buhari ta ware wa 'yan sanda kudin sayen man fetur

Kakakin rundunar 'yan sandan, Michael Abattam, ya tabbatar da harin sannan ya kara da cewa mutane biyar da suka hada da 'yan sanda biyu da 'yan daba uku sun mutu a harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abattam ya ce:

“A ranar 13 ga watan Agusta, da misalin karfe 02:45 na dare, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai da ake zargi mambobin kungiyar ta’addanci ta IPOB/ ESN, sun zo da yawan su don kai hari ofishin ‘yan sanda na Izombe amma ba su samu damar shiga ofishin ba saboda hanzarin mayar da martani da rundunar 'yan sandan Imo suka yi.
“‘ Yan bindigar da suka ga ‘yan sanda sun yi artabu da su sun yi nasara, saboda karfin wutar da’ yan sandan suka samu. Sai suka gudu zuwa cikin daji kuma ana cikin haka ne aka kasha uku daga cikin bandan bindigar sannan aka kwato makansu.

Kara karanta wannan

IPOB: An kashe jami'ai 4 a yayin da 'yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda

“Yayin da sauran suka arce cikin daji da raunukan harsashi. Abin takaici, rundunar ta rasa manyan jami’anta biyu a harin.”

Sojoji sun hallaka yan ta'addan IPOB 6, an damke 13, an kwace AK47 guda 19

A wani labarin, rundunar Sojojin Najeriya tare da hadin kan sauran jami'an tsaro a kudu maso gabas inda suka hallaka kwamandan IPOB da yaransa biyar bayan artabu da sukayi a Nkanu, jihar Enugu.

Hakazalika jami'an sun damke mutum 13 cikin yan kungiyar rajin ballewa daga Najeriya.

Mukaddashin diraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai kan nasarorin da suka samu ranar Alhamis, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel