APC da PDP duk daya ne, in ji tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe

APC da PDP duk daya ne, in ji tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe

  • Wani fitaccen jigo a jam'iyyar PDP, Doyin Okupe, ya ce babu wani babban bambanci tsakanin jam'iyyarsa da APC mai mulki
  • Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Jonathan, ya ce da yawa daga cikin mambobin APC na yanzu ‘yan PDP ne
  • Dan siyasar da aka haifa a jihar Ogun ya kuma yi tsokaci kan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP gabanin shekarar 2023

Lagas - Doyin Okupe, tsohon babban hadimin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) duk daya ce.

A cewar dan siyasa, babu abin da ya raba jam’iyyun siyasar Najeriya guda biyu saboda kashi saba’in na mutanen da ke rike da madafun iko a APC a yau dukkansu ‘yan PDP ne.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

Najeriya: APC da PDP duk daya ne, in ji tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe
Doyin Okupe ya ce duk jirgi daya ne ya kwaso APC da PDP Hoto: Doyin Okupe
Asali: Facebook

Mista Okupe ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Agusta, lokacin da ya fito a wani shirin ARISE News na The Morning Show.

Ya ambaci gwamnan Ogun mai ci da tsoffin gwamnonin jihar a matsayin mambobin da suka rike madafun iko a PDP amma yanzu suka tsinci kansu a matsayin jagorori a APC.

Ya ce:

"Maganar gaskiya ita ce, da kyar in akwai wani banbanci tsakanin jam'iyyun siyasar biyu. A bayyane yake. Idan yau ina PDP kuma gobe ina APC toh ba mutum daya ba ne ...
"Kashi hamsin cikin dari na wadanda ke rike da madafun iko a APC a yau, in ba 70% ba, duk mutanen PDP ne."

Ya kuma ce gaba daya hayaniyar jami’an kasa da suka yi murabus daga PDP, da kuma rikicin da APC ke fama da shi, kawai yunkuri ne zuwa zaben 2023.

Kara karanta wannan

Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Hamayya YPP

APC da PDP duk jirgi daya ne: Jega ya gargadi 'yan Najeriya cewa su guje masu

A baya, tsohon shugaban hukumar INEC, farfesa Attahiru jega ya gargadi 'yan Najeriya kan sake zaban shugabanni daga jam'iyyun APC da PDP.

A cewarsa, wadannan jam'iyya dukkansu hali daya suke tafe akai, kuma babu abinda suka taba wa 'yan Najeriya tsawon shekaru 20 da suka yi suna mulki.

Jega ya bayyana haka ne yayin wata hira da sashin Hausa na BBC, wanda Legit Hausa ta tattaro yana cewa, babu bukatar sake yin imani da jam'iyyun a nan gaba kasancewar sun gagara cimma wani abin kirki tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng