2023: Tinubu zai zama shugaban kasa nagari, in ji tsohon hadimin Jonathan, ya fadi dalili

2023: Tinubu zai zama shugaban kasa nagari, in ji tsohon hadimin Jonathan, ya fadi dalili

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe yayi magana akan karfin da fitaccen jigon APC Tinubu ke da shi na mulkin Najeriya
  • Okupe wanda babban hadimin shugaban kasa ne a lokacin gwamnatin Jonathan ya ce Tinubu zai zama shugaba nagari
  • Sai dai, likitan da ya zama dan siyasa, ya ce bai sani ba ko shugaban APC zai samu damar zama shugaban kasa

Lagos, Nigeria - Dr Doyin Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, zai yi rawar gani idan ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Arise News a ranar Juma’a, 13 ga watan Agusta, Okupe yace Tinubu, tsohon gwamnan na jihar Legas, zai zama shugaba nagari.

Kara karanta wannan

Ni fa sulhu kawai naje yi: Tsohon gwamna Bindow ya kare kansa kan zaman sukar Buhari

2023: Tinubu zai zama shugaban kasa nagari, in ji tsohon hadimin Jonathan, ya fadi dalili
Dr Doyin Okupe ya ce Tinubu zai yi kokari idan ya zama shugaban kasar Najeriya Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Da aka tambaye shi wadanda zai yi la’akari da su idan zai yi jerin gwanayen ‘yan siyasa masu iya mulkin kasar nan, likitan da ya koma dan siyasa ya ce:

"Bola Tinubu, a wurina, zai zama shugaba nagari. Na yi imani da haka. Na yi hulda da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wata rana na zauna tare da Bola Tinubu shekaru da yawa da suka gabata kuma ranar Asabar ce kuma babu kowa a wurin na kusan awanni huɗu kuma mun yi magana.
"Daga wannan ranar, nake girmama mutumin. Yana da nasa matsalolin, yana da nasa kurakuran amma na yi imanin idan ya samu dama zai iya yin kokari. Na yi imani da haka.
"Ko zai samu dama ko ba zai samu ba, ban sani ba."

Ni ne wanda IBB yake burin ya zama Shugaban kasa inji Tsohon Hadimin Jonathan, Obasanjo

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

A gefe guda, tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Doyin Okupe ya ce shi ne ya fi dace wa da ya dare a kan kujerar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa.

Doyin Okupe yake cewa shi tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida Babangida yake da shi a rai da yake maganar wanda ya dace da mulki.

Da aka yi hira da shi a Arise TV dazu, Doyin Okupe yace babu shakka Ibrahim Badamasi Babangida shi ya hango da yake batun siyasar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng