An Fara Zargin Kudin Mutumin Tinubu, Ya ba Kamfen Dinsa Motoci 600 Na N3.6bn

An Fara Zargin Kudin Mutumin Tinubu, Ya ba Kamfen Dinsa Motoci 600 Na N3.6bn

  • Government Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayar da motoci 633 da aka kiyasta kuɗinsu ya kai Naira biliyan 3.68
  • Rahoto ya ce ƙimar motocin ta haura iyakar Naira miliyan 500 da Dokar Zaɓe ta 2026 ta gindaya wa gudummawar mutum ɗaya
  • INEC ta ce sai an kai batun kotu kafin a iya tantance ko dokar ta shafi gudummawar da ba kuɗi ba, kamar motoci da sauran kayayyaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

ABUJA — An fara nuna damuwa kan gudummawar motoci da tsohon shugaban ’yan bindigar Neja Delta, Government Ekpemupolo ya ba Bola Tinubu.

Mutumin wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayar domin tallafa wa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Tompolo ya ba kamfen Tinubu motoci
Tulin motocin da Government Tompolo ya ba kamfen shugaba Bola Tinubu. Hoto: @Djjidexx1, @officialABAT.
Source: Twitter

Motocin da Tompolo ya ba kamfen Tinubu

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ɗauki darasi, ta sauya tsarin da za ta yi amfani da shi a zaɓen 2027

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Tompolo, wanda shi ne babban jagoran ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement, ya bayar da motoci sama da 600 waɗanda ƙimarsu ta kai kusan Naira biliyan 3.68.

Tompolo ya ba da wannan gudummawa ne domin tallafa wa sake zaɓen Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC.

Rahoton ya nuna cewa ƙimar motocin ta haura iyakar Naira miliyan 500 da Dokar Zaɓe ta 2026 ta gindaya a matsayin gudummawar da mutum ko wata ƙungiya za ta iya bayarwa ga ɗan takara.

Sai dai Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce akwai buƙatar kotu ta fassara dokar domin tantance ko iyakar ta shafi gudummawar kayayyaki da ba kuɗi ba.

Motoci 633 da aka raba a jihohi

Bincike ya nuna cewa Tompolo ya raba motoci 633 aƙalla jihohi 21 na Najeriya ta hannun ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement.

Motocin sun haɗa da ƙananan motoci kirar Opel Zafira 583 da motocin bas kirar Sharon 50, waɗanda aka kiyasta jimillar ƙimarsu ta kai Naira biliyan 3.68.

An yi amfani da matsakaicin farashin Opel Zafira na Naira miliyan 5.5 da kuma Naira miliyan 9.5 na kowace motar Sharon wajen ƙididdige kuɗin.

Kara karanta wannan

'Zan ba kowace mazaba N40m': Ɗan takarar shugaban ƙasa ya ɗauki alƙawari

Rahoton ya ce Kano ce ta samu motoci 50 da aka kiyasta kuɗinsu ya kai Naira miliyan 275, sai Borno mai motoci 44 da aka ƙiyasta kuɗinsu ya kai Naira miliyan 242.

Yobe ta samu motoci 40 da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 220, yayin da Katsina ta samu 34 da aka kiyasta kuɗinsu ya kai Naira miliyan 187.

Sauran jihohin da suka samu motocin sun haɗa da Bauchi, Kwara, Jigawa, Imo, Osun, Sokoto, Ondo, Gombe, Ogun, Plateau, Taraba, Enugu, Cross River da Zamfara.

Nasarawa ce ta samu motocin bas kirar Sharon guda 50 da aka kiyasta ƙimarsu ta kai Naira miliyan 475.

Abin da dokar zaɓe ta tanada kan haka

Sashe na 92(8) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya tanadi cewa mutum ko wata ƙungiya ba za ta bayar da gudummawar da ta haura Naira miliyan 500 ga ɗan takara ba, cewar Punch.

Haka kuma, sashe na 92(10) ya tanadi cewa mutumin da ya bayar da gudummawar da ta wuce iyakar zai iya fuskantar tarar da ta ninka adadin kuɗin da ya wuce sau biyar.

Sai dai rahoton ya ce babu wata hujja da aka bayyana a bainar jama'a da ke nuna cewa Tompolo ya bayar da kuɗi sama da Naira miliyan 500 kai tsaye ga yaƙin neman zaɓen Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Tompolo ya shiga Arewa da motocin Tinubu

An ji cewa Attajirin Kudancin Najeriya da aka sani da Tompolo, ya kaddamar kungiyar tallata Bola Tinubu a jihar Katsina domin tara goyon bayan jama’a ga sake zabensa a 2027.

Tompolo, wanda ya kafa kuma ke jagorantar kungiyar, ya zabi Katsina a matsayin jihar farko da za a fara kaddamar da shirin a Arewa, inda aka nada shugabanni.

An raba motoci 34 na yakin neman zabe ga masu kula da kananan hukumomi 34 domin taimakawa wajen gudanar da yakin neman goyon bayan Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.