Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi

Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanal ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi

  • An bayyana rahoton cewa an kashe marigayi Kanal Ibrahim Sakaba ne saboda ya ƙi satar kuɗi a matsayin na bogi
  • Rundunar Sojin Najeriya ta ce zargin da aka alakanta da uwargidan babban jami'in, Misis Oluwaseun Sakaba bai da wani makama
  • Kakakin rundunar, Brig-Gen. Onyema Nwachukwu ya karyata labarin, yana mai cewa Sakaba ya mutu yana yiwa kasa hidima

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata wata kasida da ke ikirarin cewa an kashe marigayi Kanal Ibrahim Sakaba ne saboda kin satar kudaden da aka ware don yakar Boko Haram.

Legit.ng ta tattaro cewa wannan bayani ya fito ne daga mai magana da yawun rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, kuma ya wallafa a Facebook.

Rundunar sojin Najeriya ta yi martani yayin da matar marigayin kanar ta yi ikirarin cewa kashe mijinta aka yi
Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani kan ikirarin Misis Oluwaseun Sakaba, matar marigayi Kanar Ibrahim Sakaba Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A cewar Nwachukwu, Sakaba, kamar sauran hafsoshi da sojoji sun biya mafi girman farashi a yakin da ake yi da ta'addanci, ya kara da cewa mutuwarsa tana da zafi ga NA kuma babban rashi ne.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Ya ci gaba da lura da cewa hasashen duk wani abu da ya saba ba karamin illa bane ga kasarmu da sadaukarwar sojoji.

Mai magana da yawun rundunar ya yi bayanin cewa Misis Sakaba ta yi tsokaci kan ikirari mara tushe da makama ba tare da wata hujja ba.

Ya ce sojojin ba za su so su shiga cikin matsala da kowa ba duba ga dimbin sadaukarwar da sojoji suka yi, sai dai, yana da mahimmanci a magance tuhumar da aka alakanta da matar marigayin.

Nwachukwu ya bayyana marigayin a matsayin babban jami'in da ake girmamawa wanda ya ba da komai nasa wajen kare 'yancin da dan Najeriya ke morewa a yau.

A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya yi wa Hadiza Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa, tana da shekaru 80 a duniya.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Yi Wuf da Matar Dalibinsa Daga Zuwa Neman Albarkar Aure

Wata sanarwa da ‘dan tsohon shugaban kasar, Bala Shagari ya fitar, ya bayyana cewa ta mutu ne sakamakon cutar korona a cibiyar killace masu cutar da ke Gwagwalada.

Ya kuma bayyana cewa za a yi jana’izarta a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta, bayan sallar la’asar a babban masallacin kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng