A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan

A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan

  • Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna godiya ga shugaba Buhari kan ziyarar da ya kai masa
  • Buhari a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta ya ziyarci Tinubu a Landan yayin da ake rade-radin cewa shugaban na APC yana fama da rashin lafiya
  • Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce ziyarar da Buhari ya kai ta nuna halinsa na kulawa

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna matukar godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan a ranar 12 ga watan Agusta, jaridar Thisday ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaba Buhari ya yi a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, ya ziyarci Tinubu a lokacin da yake kasar Ingila.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida bayan kimanin makonni biyu a Landan

Tinubu ya aika muhimmin sako ga Shugaba Buhari kan ziyarar da ya kai masa a birnin Landan
Tinubu ya yi godiya ga Shugaba Buhari kan ziyarar da ya kai masa a birnin Landan Hoto: @Bashamad
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa daga ofishin yada labarai na jiya ya ce:

“Ziyarar ta sada zumunci ce kuma abun so wacce ta jaddada mutunci da kulawar Shugaban kasarmu kuma Babban Kwamandan mu.
“Da wannan karimcin, Shugaban kasa ya sake nuna irin tunaninsa da tawali'u; ya bijirewa sharhin da masu sukarsa suka yi.
"Asiwaju yana sake godewa Shugaba Buhari da ya dauki lokaci don ya ziyarce shi kuma baya yiwa Shugaban kasar fatan komai face na alkhairi yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da gudanar da mulki da jagorancin al'umma."

Shugaba Buhari ya kai wa jagoran APC, Bola Tinubu ziyara har gidansa a Landan

A baya mun kawo cewa, mai girma shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara dakansa zuwa gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Landan, kasar Ingila.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

Mai taimaka wa shugaban Najeriya a kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad ya fitar da hotunan wannan gana wa da aka yi tsakanin manyan kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari, Muhammadu Buhari ya ziyarci tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel