Matar tsohon shugaban kasa, Hadiza Shagari ta mutu bayan fama da cutar korona
- Matar marigayi tsohon Shugaban kasa, Hadiza Shehu Shagari ta amsa kiran Allah
- Hajiya Hadiza ta rasu a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta bayan ta yi fama da cutar korona
- Za a yi jana'izarta bayan sallar La'asar a babban masaLlacin kasa da ke Abuja
Allah ya yi wa Hadiza Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa, tana da shekaru 80 a duniya, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Wata sanarwa da ‘dan tsohon shugaban kasar, Bala Shagari ya fitar, ya bayyana cewa ta mutu ne sakamakon cutar korona a cibiyar killace masu cutar da ke Gwagwalada.
Ya kuma bayyana cewa za a yi jana’izarta a yau Alhamis, 12 ga watan Agusta, bayan sallar la’asar a babban masallacin kasa da ke Abuja, Solacebase ta ruwaito.
Sanarwar ta zo kamar haka:
“Mun rasa ta da sanyin safiyar yau, 12 ga watan Agusta 2021, da misalin karfe 3:00am, bayan ta yi fama da Covid-19 a Cibiyar Killace masu ita na Gwagwalada da ke Abuja.
“Hajiya Hadiza Shehu Shagari ta na da shekaru 80 a duniya. Za a yi Sallar Jana'izarta a yau, da karfe 4:00 na yamma bayan sallar la’asar, a Masallacin Kasa, Abuja.”
A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta ce bata shirya kafa wani sabon dokar kulle ba duk da dawowar cutar COVID-19 a fadin tarayya.
Channels TV ta ruwaito cewa ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 12 ga Agusta, a taron mako-mako na hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, Abuja.
Legit.ng ta tattaro cewa Ministan yace adadin mutanen da suka kamu bai kai a kakaba sabuwar dokar kulle ba.
Asali: Legit.ng