'Yan Bindiga Sun Kai Harin da Jawo Asara Mai Girma a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kai Harin da Jawo Asara Mai Girma a Sokoto

  • ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Dukkuma da ke Sabon Birni ranar Talata da dare, inda suka yi garkuwa da mutum shida
  • Hatsabiban 'yan bindiga sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu yawa na mutanen kauyen da suka kai
  • Harin ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankunan gabashin Sokoto, waɗanda ke fuskantar matsalar garkuwa da mutane da satar dabbobi akai-akai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida tare da satar adadin awaki da tumaki da ba a bayyana ba a wani hari da suka kai a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun yi ta'asar ne yayin wani hari da suka kai ƙauyen Dukkuma da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto Hoto: Dr. Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Rahotan jaridar The Punch ya bayyana cewa maharan sun kai harin ne a daren ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba kan lafiyar ’yan uwansu da kuma ƙara taɓarɓarewar tsaro a yankunan karkara.

Kara karanta wannan

Mazan fama: Amurka ta yabawa sojojin Najeriya bayan gudanar da wani gagarumin aiki

’Yan sanda sun tabbatar da sace mutum shida

Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewa mutum shida ne aka yi garkuwa da su a harin, tare da musanta wani rahoto na farko da ya ce an sace mutum 14.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmed Rufai, ne ya bayyana hakan lokacin da Legit Hausa ta tuntube shi domin samun karin bayani a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2026.

"An yi garkuwa da mutum shida, yayin da aka sace adadin awaki da tumaki da ba a tantance ba.” In ji shi.

Wannan bayani ya fayyace adadin mutanen da aka tabbatar an sace, sabanin rahoton farko da ya bayyana cewa mutum 14 ne suka faɗa hannun maharan.

Mazauna gabashin Sokoto na cikin fargaba

Wannan sabon hari ya ƙara dagula hankalin mazauna Sabon Birni da sauran al’ummomin gabashin jihar Sokoto, waɗanda suka sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga, sace mutane da kuma satar dabbobi.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Matashi ya mutu a ƙoƙarin kare iyayensa daga sharrin 'yan bindiga

Mazauna yankunan da abin ya shafa na ci gaba da rayuwa cikin fargabar yiwuwar sace su ko rasa ’yan uwansu, tare da asarar dabbobin da suke dogaro da su wajen gudanar da rayuwarsu.

A wasu lokuta, iyalai kan shafe kwanaki cikin rashin tabbas, ba tare da sanin halin da ’yan uwansu da aka yi garkuwa da su suke ciki ba.

An kai wani hari a jihar Sokoto

Wannan sabon lamari ya faru ne bayan wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen Yartsakuwa da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

An ce maharan sun mamaye ƙauyen ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba, lamarin da ya ƙara nuna yawaitar hare-haren da al’ummomin jihar ke fuskanta.

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Buratai ya yi magana kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hafsan sojojin kasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bayyana cewa ƙarfin soji kaɗai ba zai iya kawo ƙarshen ta’addanci ba.

Janar Buratai ya buƙaci gwamnati ta zuba jari sosai a fannin ilimi domin haɓaka tunanin matasa da basirarsu, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a dogon lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng