Shinkafa da Wake: An Kafa Kwamitin Kamfen Tinubu da APC Cike da Yan Adawa
- Jam’iyyar APC ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 350 domin shirya zaɓen 2027
- An naɗa Chief Azuka Okwusa a matsayin darakta-janar, yayin da shugaban APC na jihar, Sanata Emmanuel Anosike, zai jagoranci kwamitin
- Jam’iyyar ta umarci mambobin kwamitin su gudanar da gangamin gida-gida a rumfunan zaɓe 5,526 domin tallafa wa Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Jam’iyyar APC a jihar Anambra ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 350 domin tsara dabarun neman goyon baya da kuma shirya tunkarar zaɓen 2027.
An ƙaddamar da kwamitin ne a sakatariyar jam’iyyar da ke Awka ranar Laraba, inda aka naɗa Chief Azuka Okwusa a matsayin darakta-janar, yayin da shugaban APC na jihar, Sanata Emmanuel Anosike, zai zama shugaban kwamitin.

Source: Twitter
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Obiora Okpara a matsayin sakatare, Dr Valentine Ilobi a matsayin shugaban sashen yaɗa labarai, Mark Okoye na jam’iyyar APGA, Emeka Agbasi da Dr Pascal Candle, cewar Punch.

Kara karanta wannan
An kafa kwamitin yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar ADC
Haka kuma, tsohon ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Dr Chris Ngige, da ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen 2025, Prince Nicholas Ukachukwu, an naɗa su a matsayin masu kula da kwamitin.
APC ta fara shirin yaƙin neman zaɓen Tinubu
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kwamitin, Anosike ya buƙaci mambobinsa su ƙara ƙaimi wajen neman goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2027.
Ya ce ya kamata jam’iyyar ta mayar da hankali kan nasarori da ayyukan gwamnatin Tinubu wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maimakon amfani da ra'ayoyin siyasa kawai.
Anosike ya bayyana cewa babban dalilin kafa kwamitin shi ne fara gangamin neman zaɓe gida-gida a rumfunan zaɓe 5,526 da ke jihar Anambra.
Ya ce:
“Babban dalilin ƙaddamar da kwamitin shi ne fara gangamin neman zaɓe gida-gida a dukkan rumfunan zaɓe 5,526 da ke jihar Anambra.”

Source: Original
An shirya karbar Tinubu a Anambra
Shugaban jam’iyyar ya kuma bayyana cewa APC a ƙarƙashin jagorancinsa ta shirya tarbar Shugaba Tinubu zuwa jihar domin gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen sake zaɓensa a ranar 19 ga Nuwamba a filin Alex Ekwueme Square da ke Awka.
Ya buƙaci mambobin kwamitin su mayar da hankali kan neman goyon bayan jama'a a matakin ƙasa, tare da kasancewa a rumfunan zaɓensu har zuwa lokacin kammala zaɓen shekara mai zuwa, cewar Vanguard.
An saka gwamnan adawa a kamfen Tinubu
Mun ba ku rahoton cewa jam’iyyar APGA ta taya Gwamna Chukwuma Soludo murnar naɗa shi a kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu.
APGA ta ce naɗin Soludo ya nuna kyakkyawar alaƙarta da gwamnatin tarayya, tare da bayyana cewa za ta goyi bayan Tinubu.
Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta goyi bayan Tinubu shugaban ƙasa, yayin da take son ‘yan takararta su lashe kujerun majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng
