Kwamishinan Neja da aka sako ya bayyana wadanda suka sace shi

Kwamishinan Neja da aka sako ya bayyana wadanda suka sace shi

  • Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja da aka sako, Alhaji Muhammad Sani Idris, ya magantu a kan yan bindigar da suka sace shi
  • Idris ya bayyana cewa abokan hamayya ne suka yo hayar 'yan bindigan daga Zamfara domin su yi garkuwa da shi
  • Sai dai ya bayyana cewa shi ya yafe wa maharan domin sun yi alkawarin daina fashi saboda shi

Jihar Neja - Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja da aka sace, Alhaji Muhammad Sani Idris, ya ce 'yan bindigan Zamfara da abokan gaba suka yo haya ne aka yi garkuwa da shi.

Da yake magana jim kadan bayan sakin nasa, ya ce an ce masu garkuwar da su kashe shi idan ya ki biyan kudin fansa na N200m, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan Neja da aka sako ya bayyana wadanda suka sace shi
Kwamishinan Neja da aka sako ya ce ya yafe wa wadanda suka sace shi Hoto: Office Of The Chief Press NGS - Mary Noel Berje
Asali: Facebook

Ya ce:

“Mutanen da suka sace ni, don Allah kar ku la’ancesu domin kafin na bar su na fada musu na yafe masu.
“Sun yi alkawarin cewa za su daina yin fashi saboda ni.
“Ba su san wannan ƙauyen ba amma an ɗauke su aiki ne daga Jihar Zamfara don sace ni.
“Sun ce a kowane wata, gwamnan jihar Neja yana ba ni N200m kuma idan na ba su kasa da N200m, a kashe ni. Na gafarta ma masu garkuwar da mutanen da suka yi hayar su."

Idris, wanda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi da sanyin safiyar ranar Litinin daga gidansa da ke unguwar Babban-Tunga da ke kan babbar hanyar Abuja/Kaduna a jihar, ya dawo unguwar da misalin karfe 9:30 na daren Alhamis

Kwamishinan bai bayyana ko an biya kudin fansa ba.

Batun sace kwamishinan Neja: Gwamnati ba za ta tattauna da miyagu ko biyansu fansa ba

A baya mun ji cewa iyalan kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun fara tattaunawa da wadanda suka sace kwamishinan, gwamnatin jihar ta ce.

Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa wadanda suka sace kwamishinan sun tuntubi dangin inda a lokacin suka nemi N500m.

Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya fada wa THISDAY a wata hira ta wayar tarho jiya Laraba 11 ga watan Agusta cewa dangin ba za su iya biyan irin wadannan makudan kudaden da ake nema ba, “don haka suna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel