Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

  • Jam'iyyar All Progressives Congress mai mulki a Najeriya tayi Allah wadai da kiraye-kirayen a tsige shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni
  • Mai magana da yawun jam'iyyar James Akpanudoedehe ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta
  • Akpanudoedehe ya bayyana matakin kotun a matsayin mara ma’ana kuma wanda bai dace ba, yana mai cewa babbar jam'iyyar adawa tana cikin mawuyacin hali

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tayi Allah wadai da karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar akanta da shugaban kwamitin rikonta, Gwamna Mai Mala Buni.

A cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, mai magana da yawun jam’iyyar, James Akpanudoedehe, ya ce babbar jam’iyyar adawa tana aiwatar da farfaganda mara kyau.

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo
APC ta bukaci jam'iyyar PDP da ta mayar da hankali a kan rigimar da yayi mata katutu a gidanta Hoto: APC
Asali: Facebook

Kodayake ya bayyana cewa APC ba za ta yi magana kan matakin zuwa kotu da PDP ta dauka ba, amma ya nemi jam’iyyar adawar da ta mayar da hankali kan rikicin da ke cikin sansaninta.

Kara karanta wannan

Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

A cikin takardar sammaci mai shafuka hudu da aka shigar a kotun a ranar Alhamis, an bukaci kotun da ta sa gwamnan ya bayyana a gabanta tare da kare ko ya tashi daga matsayin gwamna ta hanyar yarda ya zama Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC.

Akpanudoedehe, ya bayyana cewa zai zama son zuciya yin magana kan matakin da jam'iyyar adawa ta ɗauka.

PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

A baya mun ji cewa an gurfanar da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni a kotu kan nadinsa a matsayin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, ta shigar da kara na neman a cire Buni daga mukaminsa na gwamnan Yobe.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: PDP ta bukaci a gaggauta tsige Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe

Legit.ng ta tattaro cewa a cikin karar da aka shigar a ranar 12 ga watan Agusta, PDP ta gabatar da cewa Buni ya sabawa sashe na 183 na kundin tsarin mulki lokacin da ya yarda yayi aiki a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na APC duk da cewa yana rike da mukamin gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel