'Iran na Shirin Shiga Amurka Ta Dasa Bama Bamai Ta Kashe Makusanta Trump'
- Jami’an leƙen asirin Amurka sun gano wasu bayanai da ke nuna cewa Iran na shirin kai hari kan manyan jami’an gwamnatin Donald Trump a Washington
- Rahoton leƙen asirin ya nuna cewa Iran na nazarin amfani da bam mai yaɗa sinadaran rediyo ko makamin sinadarai wajen kai harin
- Sai dai jami’an Amurka sun ce ba a tabbatar da cewa Iran ta yanke shawarar aiwatar da harin ko kuma tana da mutanen da za su iya kai shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Wasu bayanan leƙen asirin Amurka sun nuna cewa Iran na ƙirƙiro shirin kai hari kan manyan jami’an gwamnatin Shugaba Donald Trump ta hanyar amfani da bam mai yaɗa sinadaran rediyo ko makamin sinadarai a Washington DC.
Jami’an gwamnatin Amurka bakwai ne suka bayyana wannan batu, inda suka ce bayanan sun nuna wurare da kuma mutanen da ake iya kai wa harin.

Source: Facebook
CNN ta wallafa cewa majiyoyin sun bayyana cewa a yanzu shirin na iya kasancewa wani yunƙuri ne na Iran na tanadar da hanyoyin da za ta iya amfani da su, ba wai alamar cewa harin na gab da faruwa ba.
Amurka na bibiyar shirin Iran
Jami’an Amurka sun ce bayanan da suka samu sun haifar da tarurruka da dama a makon da ya gabata domin tsara hanyoyin da za a bi wajen dakile duk wani yunƙurin kai harin.
Kakakin fadar White House, Lauren Bis, ta ce Amurka na sanya ido kan duk wata barazana da za ta iya tasowa, amma a halin yanzu babu wata sahihiyar barazanar kai hari cikin ƙasar.
Duk da haka, jami’an Amurka na kallon bayanan a matsayin abin damuwa, musamman ganin matsin lambar da Iran ke fuskanta sakamakon hare-haren sojin Amurka da kuma takunkumin tattalin arziki da aka kakaba mata.
Ynet News ta rahoto wata majiya ta ce har yanzu ana muhawara kan ko Iran tana da mutanen da za su iya aiwatar da harin a cikin Amurka.

Source: Getty Images
Yadda bam din ke aiki
Bam mai yaɗa sinadaran rediyo, wanda ake kira Dirty Bomb, makami ne da ake haɗa sinadaran rediyo da bam na yau da kullum domin yaɗa gurɓatattun sinadarai a wurin da aka tayar da shi.
Jami’an Amurka sun yi gargaɗin cewa ƙasar na iya fuskantar haɗarin irin wannan hari saboda ba shi da wahalar haɗawa kamar wasu manyan makamai.
Sun ce Iran ba lallai sai ta shigo da ƙwararrun mayaƙanta cikin Amurka ba, domin tana iya neman wani mutum da ke zaune a ƙasar ya aiwatar da harin.
Wani jami’in leƙen asirin ya bayyana cewa Amurka ta gano wasu saƙonni da ke nuna cewa Iran na ikirarin ta ɓoye kayayyakin ƙera bam a cikin ƙasar.
Trump zai tafi China
A wani labarin, kun ji cewa fadar White House ta sanar da shirin ganawar Shugaban Amurka, Donald Trump, da takwarorinsa na Rasha da China, Vladimir Putin da Xi Jinping a China.
Kakakin fadar White House, Olivia Wales, ta ce shugabannin ƙasashen uku za su tattauna batutuwa daban-daban, ciki har da rage yawan makaman nukiliya a duniya.
Ana kuma sa ran batun Iran zai iya kasancewa cikin abubuwan da za su tattauna, amma ba a sa ran za su tattauna yaƙin Ukraine da Rasha.
Asali: Legit.ng


