Ban nemi kotu ta kori Buni a matsayin Gwamnan Yobe ba - Dan takarar gwamnan PDP

Ban nemi kotu ta kori Buni a matsayin Gwamnan Yobe ba - Dan takarar gwamnan PDP

  • Dan takarar gwamnan jihar Yobe na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Ambasada Umaru Damagum yace bai nemi kotu ta tsige Gwamna Mala Buni daga kujerarsa ba
  • Damagum ya jadadda cewa shima a labarai kawai ya gani yayin da yake kallon talbijin a daren jiya
  • Sai dai ya zargi wasu 'ya'yan PDP da fusatattun 'yan APC da shigar da karar domin tayar da hankali Buni

Dan takarar gwamnan jihar Yobe na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Ambasada Umaru Damagum ya nisanta kansa daga karar da ke neman a tsige gwamna Mai Mala Buni.

Damagum ya shaida wa The Nation a wata hira ta musamman a Damaturu cewa ya sami labarin karar ne kawai a lokacin da yake kallon labarai jiya da karfe 8:00 na dare.

Kara karanta wannan

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

Ban nemi kotu ta kori Buni a matsayin Gwamnan Yobe ba - Dan takarar gwamnan PDP
Dan takarar gwamnan PDP a zaben 2019 yace shima a labarai ya gani cewa an maka Gwamna Buni a kotu Hoto: APC
Asali: Original

Tsohon Jakadan Najeriya a Romania da Bulgaria ya kara da cewa bai tuntubi ko yi wa wani lauya bayani don shigar da wata shari’a a madadinsa kan batun da ake magana akai ba.

Ya yi zargin cewa wasu mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da suka fusata bayan babban taron mazabu na karshe da wasu 'yan PDP na iya zama sune suka shigar da karar don tayar da hankalin Gwamna Buni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina tsammanin wasu mambobin jam’iyyata ta PDP ba su yi farin ciki da nasarar babban taron jihar na karshe da muka yi ba a jihar.

Ya ce:

“Don saninku, akwai shari’ar kotu a Babbar Kotun Damaturu kuma ina zargin wata dabara ce ta karya wannan shari’ar.
“Ina kuma tsammanin wannan na iya fitowa daga membobin APC da kansu duba ga yadda aka hadewa Gwamna Buni kai a yankin.”

Kara karanta wannan

Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

Jigon na PDP ya bayyana cewa ya nemi lauyansa da ya binciki duk wanda ke da hannu a karar sannan ya dawo gare shi, inda ya yi alkawarin bayar da karin bayanai da rana.

A cewarsa: "Abin dariya ne cewa wadanda suka shigar da wannan karar ba su san cewa abokin takarar nawa ya dade da komawa APC ba.”

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

A gefe guda, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tayi Allah wadai da karar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar akanta da shugaban kwamitin rikonta, Gwamna Mai Mala Buni.

A cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook a ranar Alhamis, mai magana da yawun jam’iyyar, James Akpanudoedehe, ya ce babbar jam’iyyar adawa tana aiwatar da farfaganda mara kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel