Shugabancin 2023: A karshe Wike ya magantu kan Atiku, yace bai san kudirin tsohon mataimakin shugaban kasar ba

Shugabancin 2023: A karshe Wike ya magantu kan Atiku, yace bai san kudirin tsohon mataimakin shugaban kasar ba

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa bai da kowani mugun nufi a kan tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar
  • Kwanan nan Atiku ya ziyarci Wike a Fatakwal, wani ci gaban da ya haifar da rade-radin cewa gwamna ya amince da tsohon mataimakin shugaban kasar
  • Sai dai kuma, da yake martani kan rade-radin, Wike ya ce bai da masaniya kan cewa Atiku na da ra’ayin takara a 2023

Fatakwal, Ribas - Biyo bayan hasashen cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya fara shirin zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya mayar da martani.

Jaridar PM News ta rahoto cewa Wike a ranar Juma'a, 13 ga watan Agusta, ya ce ba ya da masaniyar cewa tsohon mataimakin Shugaban kasar yana son tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

Shugabancin 2023: A karshe Wike ya magantu kan Atiku, yace bai san kudirin tsohon mataimakin shugaban kasar ba
Gwamna Nyesome Wike yace bai san Atiku na neman takara ba a 2023 Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa ya yi wannan ikirarin yayin da yake magana a matsayin bako a shirin Talabijin na AIT, Focus Nigeria, a Fatakwal.

Gwamnan ya ce ba shi da masaniya game da matakin Atiku saboda har yanzu PDP ba ta raba kujerar shugaban kasa ba.

Gwamna Wike ya ce ba shi da wata matsala da Atiku da Secondus

Wike ya kuma ce warware rikicin cikin gida da ke girgiza Jam’iyyar PDP ya kawar da fargabar da yake yi na yiwuwar kutsawa cikin jam’iyyar.

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito cewa Wike ya bayyana cewa irin yadda gwamnonin PDP da mambobin kwamitin amintattu suka warware rikicin ya karfafa burin yan Najeriya cewa jam'iyyar a shirye take ta karbe mulkin daga hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Tana shirin kwabewa yayin da PDP ta nemi kotu ta tsige Buni a matsayin gwamnan Yobe

Gwamnan ya yi bayanin cewa ba sabon abu bane wata jam’iyya ta fuskanci rigingimun cikin gida duba da zabe mai zuwa da kuma ra’ayoyi daban -daban, amma ya yabawa gwamnonin PDP kan haduwa don yin magana da murya daya don kawo karshen sabanin.

Wike ya yi watsi da rade -radin cewa yana da sabani na sirri da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya kara da cewa babban abin da ya fi damunsa shi ne kubutar da PDP daga halaka.

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja IBB ya yi waje da Atiku, Tinubu daga zaben 2023

A baya, mun kawo cewa tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata 'yan Najeriya su zabi tsofaffin 'yan siyasa ba a 2023.

Babangida, wanda ake kira IBB, ya fada a ranar Juma'a, 6 ga watan Agusta, cewa kasar na bukatar wani matashi mai kwazo da zai karbi mulki daga hannun Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen jigon PDP ya bayyana abin da zai yi idan Tinubu ya zama shugaban kasa

A cewarsa, Najeriya tana da albarkatu na dan adam da kasa don canza kasar ba tare da taimakon kasashen waje ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel