Mutum 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin ‘yan bindiga a Kaduna
- Mutane 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin ‘yan fashi bayan jami’an tsaro sun far ma miyagun
- Gwamnatin Kaduna ce ta sanar da wannan ci gaban yayin da ta ke yabawa ayyukan tsaro a jihar
- Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na ihar ya ce mutanen sun kubuta ne daga sansanin da ke wajen garin Sabon Birni a karamar hukumar Igabi
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu mutane da aka yi garkuwa dasu su 11 sun tsere daga sansanin ‘yan bindiga yayin da ayyukan tsaro ke ci gaba a jihar, PM News ta ruwaito.
Mista Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ya tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.
Aruwan ya ce:
“Rahotanni daga hukumomin tsaro sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa mutane 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere daga sansanin ‘yan bindiga da ke wajen garin Sabon Birni na karamar hukumar Igabi ta jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram
"A cewar rahotannin, ayyukan tsaro na ci gaba da tarwatsa sansanin 'yan bindigar da yawa, wanda hakan yasa su cikin damuwa sannan ya ba mutanen da aka tsare a wurin damar kubuta.”
Aruwan ya kara da cewa binciken da aka yi ya nuna cewa mutanen 11 da aka yi garkuwar da su sun hada da wadanda aka yi garkuwa da su daga Dumbin Rauga a karamar hukumar Zariya da kuma a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya.
“An bayar da rahoton cewa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a Dutsen Abba sun biya kudin fansa na Naira miliyan uku, amma ‘yan bindigar sun saba yarjejeniya kan sakin wadanda aka yi garkuwa da su, inda suka dage cewa dole ne a saka babura biyu a cikin yarjejeniyar fansar.
"Sojojin sun gano wadanda suka tsere din kuma tuni aka sada su da iyalansu," in ji shi.
Kwamishinan ya kuma ce dakarun Operation Safe Haven sun bayar da rahoton ceto wasu mutane biyu da aka sace a kusa da kauyen Kirti na karamar hukumar Jema’a, jaridar The Cable ta ruwaito.
Ya bayyana cewa sojojin sun kuma ceto wata mata a kauyen Ungwan Sarki Goza, yankin Mariri a karamar hukumar Lere.
Ya ce 'yan bindigar sun sace matar sannan suka yi watsi da ita a lokacin da suka hango sojojin.
Gwamna El-Rufai ya jinjinawa dakarun sojojin
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna gamsuwa da ci gaban, inda ya yaba da kokarin sojoji da kuma tasirin mummunan farmakin da suka kai kan maboyar ‘yan bindiga a fadin jihar.
Ya kuma yaba da hanzarin da sojojin suka yi na ceto mutanen da aka sace a karamar hukumar Jema’a da Lere.
Batun sace kwamishinan Neja: Gwamnati ba za ta tattauna da miyagu ko biyansu fansa ba
A wani labarin, iyalan kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun fara tattaunawa da wadanda suka sace kwamishinan, gwamnatin jihar ta ce.
Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa wadanda suka sace kwamishinan sun tuntubi dangin inda a lokacin suka nemi N500m.
Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya fada wa THISDAY a wata hira ta wayar tarho jiya Laraba 11 ga watan Agusta cewa dangin ba za su iya biyan irin wadannan makudan kudaden da ake nema ba, “don haka suna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.”
Asali: Legit.ng