Shehu Sani Ya Bayyana Wadanda Suka Haddasa Rashin Tsaro da Talauci a Najeriya
- Shehu Sani ya zargi tsofaffin gwamnatoci da ’yan siyasa masu adawa da gazawa wajen magance matsalolin talauci da rashin tsaro lokacin da suke mulki
- Tsohon sanatan ya yi kira ga mazauna Kaduna su sake zaɓen Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a babban zaɓen 2027
- Ya yaba wa gwamnatin Uba Sani kan ayyukan hanyoyi, kafa jami’o’in gwamnatin tarayya da ƙoƙarin inganta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya zargi ’yan siyasa masu adawa da tsoffin gwamnatoci da gazawa wajen magance matsalolin rashin tsaro da talauci da ke addabar ’yan Najeriya.
Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da kamfen ɗin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, inda ya buƙaci mazauna jihar su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani a babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Shehu Sani ya zargi tsofaffin gwamnatoci
Tsohon ɗan majalisar ya ce waɗanda ke sukar gwamnatin yanzu sun gaza sauya fasalin ƙasar lokacin da suke da damar jagorantar Najeriya, cewar rahoton jaridar Leadership.
Ya bayyana cewa matsalolin talauci da rashin tsaro da ake fuskanta a yanzu sun samo asali ne daga gazawar gwamnatocin baya wajen magance su.
“Talaucin da muke fuskanta a yau sakamakon ayyukansu ne. Rashin tsaron da muke fuskanta a yau ma sakamakon ayyukansu ne.
“Da suna da wata dabarar ban mamaki ko ikon sauya Najeriya, da sun yi hakan lokacin da suke kan mulki. Sun kasance PDP, sun gaza. Sun kasance APC, sun gaza.” In ji shi.
Ya nemi al’ummar Kaduna su goyi bayan APC
Tsohon sanatan ya yi kira ga mazauna jihar Kaduna, musamman ’yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati, malamai da sauran ƙungiyoyin al’umma, da su fito da yawa domin nuna goyon bayansu ga ’yan takarar APC.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
Ya kuma yaba wa gwamnatin Gwamna Uba Sani, inda ya kawo ayyukan hanyoyi, kafa jami’o’in gwamnatin tarayya da ƙoƙarin inganta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a matsayin wasu daga cikin nasarorin da aka samu a jihar.
A cewarsa, kasancewar ministoci uku da jami’o’in gwamnatin tarayya guda huɗu a Kaduna, tare da inganta hanyoyin sufuri, na daga cikin nasarorin da ya danganta da gwamnatocin APC.
Ya yi magana kan damar APC a zaɓen 2027
Shehu Sani ya bayyana yawan mutanen da suka halarci ƙaddamar da kamfen ɗin a matsayin alamar goyon bayan da APC ke da shi a jihar Kaduna. Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu nasara a zaɓen da ke tafe.
Tsohon sanatan ya buƙaci masu zaɓe su sake zaɓen Tinubu da Uba Sani domin su sake yin wa’adi na biyu.
Ya jaddada cewa APC na buƙatar ci gaba da riƙe madafun iko a matakin gwamnatin tarayya da na jihar Kaduna.

Source: Facebook
Shehu Sani ya yi tonon silili ga 'yan siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan bambancin akida tsakanin jam'iyyar da ke mulki da 'yan adawa a Najeriya.
Shehu Sani ya ce da dama daga cikin 'yan siyasar da ke ɓangarorin adawa da na gwamnati a yanzu sun taɓa kasancewa abokan siyasa, suna aiki tare tare da kare muradunsu.
Asali: Legit.ng
