A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG
- An nemi gwamnatin Najeriya ta gaggauta tura tubabbun 'yan Boko Haram zuwa gonaki don yin noma
- Wannan shi ne matsayin Birgediya Janar John Sura (mai ritaya) wanda ya mayar da martani kan sabon ci gaba kan 'yan ta'adda da suka tuba
- Ya ce ya kamata a dauke su a matsayin mutanen da ke zaman gidan yari sannan kuma a sanya su cikin yanayin da ke kasa da na ‘yan sansanin gudun hijira
Tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Soji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma'a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura 'yan ta'addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.
A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'Ku dauki 'yan ta'addan Boko Haram da suka tuba a matsayin fursunonin yaki', jaridar Punch ta ruwaito.
Sura, wanda ya bayyana 'yan ta'addan da suka tuba a matsayin fursunonin yaki, ya bayar da hujjar cewa ya kamata a yi gyara ga Yarjejeniyar Geneva wacce ta ba su wasu gata kamar kariya daga duk wani aiki na tashin hankali gami da tsoratarwa, cin mutunci da sauransu.
Ya jaddada cewa ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke zaman gidan yari kuma a sanya su cikin yanayin da ke ƙasa da na ‘yan sansanin gudun hijira.
Ya ce:
"Game da 'yan Boko Haram da suka tuba, ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke cikin kurkuku tare da aiki mai tsanani.”
Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan shirin sakin manyan kwararrun masu hada bama-bamai na Boko Haram
Sanatan Borno ya ja-kunnen Sojoji a kan maida tsofaffin ‘Yan ta’addan Boko Haram ‘yan lele
A gefe guda, Ali Muhammad Ndume, Sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya yi kira ga jami’an tsaro su kawo karshen ta’addanci a Najeriya.
The Cable ta ce Sanatan na APC ya yabi sojojin Najeriya, sannan kuma ya nemi ayi maza ayi maganin masu tada kafar baya a yankin Arewa maso gabas.
Asali: Legit.ng