Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Wani mutumin kasar Malawi mai suna Francis Banda wanda ke zaune a yankin Ntcheu ya rushe gidaje biyu da ya ginawa matarsa da mahaifiyarta bayan ta rabu da shi.
Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, ya gargadi gwamnatin jihar da manyan jami’anta da su daina takewa ma’aikata yancinsu na zaben wanda suke so.
Allah ya yiwa dan tsohon ministan wasanni Solomon Dalung, Nehemiah Dalung, rasuwa a safiyar Litinin, 24 ga watan Oktoba. Ya mutu yana da shekaru 33 a duniya.
Justis Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya da ke zama a Calabar ta ayyana Bassey Otu a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na APC a jihar Cross River.
Dakarun rundunar sojin sama sun yi yayyafin bama-bamai a kan yan ta'addan ISWAP yayin da suke jerin gwano tsakanin Shettima Abbor da Galmasku a jihar Borno.
Rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata da masaniya a kan gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya yiwa 'ya'yan kasarsa game da yuwuwar kai hare-hare Abuja.
Mace mai kamar maza kwauri ne babu! Shi za a kira wannan mata da shi wacce ta auri maza bakwai kuma take juya su son ranta tare da daukar dawainiyarsu ita daya.
Jam’iyyar PDP a jihare Ribas ta fara kamfen dinta na zaben 2023 a jihar ta hanyar sakin motoci dauke da hotunan yan takararta amma babu Atiku Abubakar a jiki.
Kungiyar kiristocin APC a yankin arewacin kasar sun nemi lallai a sauya Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu gabannin zaben 2023.
Aisha Musa
Samu kari