Dandazon Yan Ta'adda Sun Sheka Lahira Yayin da Jirgin Soji Ya Musu Ruwan Bama-Bamai a Jihar Arewa

Dandazon Yan Ta'adda Sun Sheka Lahira Yayin da Jirgin Soji Ya Musu Ruwan Bama-Bamai a Jihar Arewa

  • Dakarun rundunar sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a kan yan ta'addan ISWAP a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno
  • Mayakan na jerin gwano tsakanin Shettima Abbor da Galmasku lokacin da dakarun sojin suka yi masu yayyafin wuta
  • Harin ya yi sanadiyar mutuwar gomman mayakan kungiyar ta'addancin yayin da wasu suka tsere

Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya ta yi luguden wuta a kan mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP inda ta kashe gomman yan ta’adda.

A cewar Zagazola Makama, wani mawallafi da ya karkata ga yankin Tafkin Chadi, yan ta’addan na jerin gwano ne lokacin da rundunar NAF ta farmake su.

Jirgin yaki
Dandazon Yan Ta'adda Sun Sheka Lahira Yayin da Jirgin Soji Ya Musu Ruwan Bama-Bamai a Jihar Arewa Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

An rahoto cewa lamarin ya afku ne a ranar Lahadi yayin da yan ta’addan ke jerin gwano tsakanin Shettima Abbor da Galmasku a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Daba Ɗauke Da Bindigu Sun Kai Wa Ɗan Takarar Gwamnan PDP Hari

Rahoton ya kuma kawo cewa jirgin yakin rundunar sojin sama da aka kawo kwanan nan ne ya kashe ya yi masu yayyafin bama-bamai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar TheCable ta rahoto daga majiya cewa an aiwatar da harin ne bayan bincike da aka gudanar ya nuno motoci biyu da babura da dama dauke da yan ta’addan.

Majiyar ta bayyana cewa jiragen yakin da aka tura don aikin ya yi dirar daidai a kan ayarin motocin yan ta’addan inda ya lalata motar hilux daya tare da kashe mutanen da ke ciki.

“Ruwan bama-baman ya kuma kashe wasu ‘yan ta’adda da ke kan babura yayin da sauran suka tsere,” cewar majiyar.

Ya ci gaba da cewa:

“An aiwatar da aikin ne da nufin fitar da yan ta’addan da ke harin tafkin Chadi da yankunan dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Borno: An yi Mummunar Arangama Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, An Halaka 6

Majiyar ta kuma kara da cewa rundunar soji da ke aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki za su ci gaba da kokarinsu na fitar da yan ta’adda da sauran miyagu daga yankin arewa maso gabas.

Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya

A wani labari na daban, rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata da masaniya kan gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya yi a Najeriya game da yuwuwar kai hari babban birnin tarayya Abuja.

Da yake martani ga tambayar da jaridar Leadership tayi masa a jiya Lahadi, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce bai da masaniya kan kowani barazana na tsaro.

Da aka tambaye shi game da shirin yan sanda na dakile harin, kakakin rundunar wanda bai zurfafa magana kan lamarin ba, ya amsa tambayar a takaice da "bani da masaniya".

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

Asali: Legit.ng

Online view pixel