Ina kula da su kuma ina biya masu dukka bukatunsu: In ji matar da ta auri maza 7 a cikin wani bidiyo
- Wata mata da ta auri maza 7 ta yi fallasa masu ban mamaki kan yadda take zama da mazajen ta
- Ta bayyana a wani faifan bidiyo cewa ta gina wa kowannensu gida kuma tana biya masu bukatunsu
- Ta ci gaba da bayyana yadda take tsare su daga cin amanarta
Wata mata ta yanke shawarar canza labarin aure ta wani siga da ba a san shi ba.
Matar da ba a gano ko wacece ba ta auri maza 7 ita kadai.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Wike ya bugi kirji ya bayyana abunda zai faru da PDP idan ya fice
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na @blog_street, matar da dukkan mazajen nata suka kewayeta ta bayyana cewa tana kula da bukatunsu ita kadai kuma har ta gina wa kowannensu gida.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Matar ta ci gaba da bayyana cewa ragamar komai na a hannunta kan abun da ya shafi yin jima'i domin ita ke yanke shawarar da wanda za a yi a cikinsu.
A cikin sautin da ke nuna karfin gwiwa, ta yi alfaharin cewa babu wanda ke da ikon cin amanarta a cikin mazajen. A cewarta, tana da karfin iko wanda ke taimaka mata wajan duba harkokin su.
KU KARANTA KUMA: Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar
A cikin faifan bidiyon, dukka mazajen nata sun yi shiru, sun mayar da hankali wajen shan wani jiko a cikin wani kwarya da ta riƙe.
Bidiyon ya haifar da martani daban-daban a shafukan sada zumunta.
Wasu mutane sun bayyana cewa dole mazan na karkashin sihiri ne, wasu kuma sun jinjina mata a matsayin sarauniyar gaske.
@ Daisybabyluv1 ya ce:
"Wannan ba sarauniya ba ce, wannan ita ce iya oshoromonga. Wadannan mazajen sun yi kama da wadanda aka yi wa sihiri. Suna karkashin ikon obo aiye ne. Suna bukatar addu’a."
@ Emrex47331004 ya rubuta:
"Idan wannan matar ta murƙushe ka taka ta kare."
A wani labarin, Shugaban kasan Korea ta arewa ya haramta saka damammun wanduna tare da askin banza a kasar sakamakon tsoron lalacewar tarbiyar matasa ta hanyar kwaikwayon kasashen yamma.
Hukuncin ya biyo baya ne sakamakon ganin cewa gayun zai iya janyo miyagun halayya a cikin matasan kasar, Britain Daily Express ta ruwaito.
"Dole ne mu ankare da kowacce alamar rayuwar 'yan jari hujja kuma dole mu yake su tare da kawar dasu," Rodong Sinmum, wani ma'aikaci kuma jigo a jam'iyya me mulki a kasar ya rubuta.
Asali: Legit.ng