Lokaci Ya Yi: Daga Kwanciya Barci, An Tarar da Gawar Fitaccen Jarumin Fim a Najeriya
- Jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood, Solomon Akiyesi ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Iyalansa sun bayyana cewa ya kwanta barci bayan ya fara shan maganin gyambon ciki, amma da safe aka tarar da gawarsa a Abuja
- Shugaban kungiyar AGN, Yakub Abubakar ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masana’antar fina-finai ta Nollywood
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Solomon Akiyesi, ya rasu a cikin barcinsa bayan gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya jefa masana’antar cikin jimami.
Shugaban ƙungiyar ‘yan wasan kwaikwayo ta ƙasa (AGN), Yakub Abubakar, ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026.

Source: Facebook
Jarumi Solomon Akiyesi ya mutu a Abuja

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu da ya ajiye aiki ya shiga takarar kujerar majalisar tarayya a Kano
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ‘yar marigayin ta bayyana cewa Akiyesi ya koka da ciwon kirji a daren kafin rasuwarsa, inda aka kai shi asibiti aka gano yana fama da gyambon ciki (ulcer) tare da ba shi magani.
Bayan dawowarsa gida, ya kwanta barci amma bai sake farkawa da safe ba, sai dai aka tarar da gawarsa.
“Matarsa ta yi ƙoƙarin ta tashe shi daga barci da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, amma ta yi magana bai amsa ba,” in ji shugaban AGN.
Masana’antar Nollywood ta yi rashi
Yakub Abubakar ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masana’antar fina-finai ta Nollywood, yana mai cewa ƙungiyar na alhini tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalansa.
Rahotanni sun nuna cewa an ajiye gawarsa a ɗakin ajiyar gawawwaki a babban birnin tarayya Abuja, inda ya rasu.
Abokan aikinsa sun shiga shafukan sada zumunta suna alhinin rasuwarsa, suna bayyana shi a matsayin jarumi mai ƙwarewa wanda ya taka rawa a fina-finai da zai sa a rika tunawa da shi.
Jaruma Celestina Dovigalle ta bayyana shi a matsayin mutum mai annashuwa, son nishadi da kuzari, tana mai cewa yana kawo farin ciki a duk inda ake daukar fim.

Source: Facebook
Takaitaccen bayani kan marigayin
Akiyesi ya yi fice a fina-finai kamar Desperate Ladies, Pretty Liars, Bridge of Contract, Heart of a Saint, Marry Who You Love (2016), Gen Z Wife (2024) da kuma Accidentally Us (2025)
Haka zalika marigayin ya kasance dan asalin garin Ososo da ke ƙaramar hukumar Akoko-Edo ta jihar Edo, ya fara harkar fim tun ƙarshen shekarun 1990
Ya fito a fina-finai sama da 100, inda ya yi suna a matsayin jarumi da kuma mai shirya fina-finai, kamar yadda The Natin ta ruwaito.
Tsohon dan wasan Najeriya ya mutu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan wasan gaba na Najeriya, Mike Eneramo ya riga mu gidan gaskiya a wurin atisayen motsa jiki a jihar Kaduna.
An ce Eneramo ya gamu da bugun zuciya ne a lokacin da ake tsakiyar atisayen, kuma ya rasu kafin a kai shi asibiti domin samun kulawa.
Eneramo ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a shekarar 2018 bayan ya shafe shekaru yana taka leda a ƙasashen waje, musamman a kasar Turkiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
