Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

  • Francis Banda ya shiga wani hali lokacin da matarsa ta kashe aurensu mai shekaru 13 sannan ta je ta auri wani
  • Abun da ya fi yi masa ciwo shine yadda ya sadaukar da komai nasa, ya gina gidaje biyu, daya na matar tasa, dayan kuma na mahaifiyarta
  • Saboda fusata da yayi, Banda ya farma gidajen biyu sannan ya ruguza su don daukar fansa

Wani mutumin kasar Malawi mai suna Francis Banda wanda ke zaune a yankin Ntcheu ya hau kanen labarai bayan ya rushe gidaje biyu a kokarinsa na daukar fansar yaudararsa da aka yi.

Malawi 24 ta rahoto cewa matar Banda ta rabu da shi kwanan nan don kasancewa da wani daban, lamarin da ya kona masa rai har ya kai ga ruguza gidajen da ya gina mata da surukarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Rusau
Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidan Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa Hoto: Malawi24
Asali: UGC

Banda ya shafe tsawon shekaru 13 da aure

A bisa ga wani faifan murya da ya saki, ya bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru 13 da matarsa kuma har sun haifi yara uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa a lokacin aurensu, ya gina gidaje biyu, daya na matar sannan daya a kauye na mahaifiyarta.

Duk da wannan sadaukarwa nasa, matar Banda ta fada tarkon soyayya da wani sannan ta koma rayuwa da shi.

“Da ya kai wani mataki, na yi kokarin zantawa da matata amma sai saurayin ne ya amsa wayar,” in ji Banda.

A wannan gabar ne ya fusata, lamarin da ya kai shi ga zuwa rusa gidajen da ya gina guda biyu.

Jama’a da suka ji abun da ya aikata sun kira tsohuwar matar tasa da butulu sannan sun ce sun fahimci matakin da mutumin ya dauka.

Kara karanta wannan

Shari'a: Mutane 3 da suka rayu a magarkama na tsawon shekarau, aka gano ba su da laifi

Åk Sàñdfôrè:

“Na goyi bayan abun da Francis Banda ya aikata, wace irin butulun mace ce wannan.”

Mac Douglas Soko:

“Ya san abun da yake yi. Shine marubucin sannan ya kammala aikinsa.

Dev Mak Artist:

“Ya yi kyau sosai, kuma hakan bai is aba; ya je ya dauke filin.”

Ina kula da su kuma ina biya masu dukka bukatunsu: In ji matar da ta auri maza 7 a cikin wani bidiyo

A wani labari na daban, wata mata ta yanke shawarar canza labarin aure ta wani siga da ba a san shi ba.

Matar da ba a gano ko wacece ba ta auri maza 7 ita kadai.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na @blog_street, matar da dukkan mazajen nata suka kewayeta ta bayyana cewa tana kula da bukatunsu ita kadai kuma har ta gina wa kowannensu gida.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

Asali: Legit.ng

Online view pixel