Kotu Ta bada Umarni kan Jami'in DSS da ake Zargi Ya Sace Budurwa a Jigawa
- Kotu ta bayar da umarci ga hukumar DSS ta saki budurwa ‘yar shekara 16 da ake zargi jami'inta ya sace
- Wannan na zuwa bayan gwamnatin Jigawa ta shiga lamarin wata yarinya da aka sace kuma jami'in DSS ya haihu da ita
- Alkalin kotun ta caccaki hukumar tsaron farin kaya DSS kan zargin boye jami’inta da ake tuhuma da aikata wannan mummunan abu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa –Babbar kotun tarrayya da ke zamanta a Dutse, jihar Jigawa, ta umarci hukumar tsaro ta DSS da ta saki wata matashiya, Walida Abdulhadi, ba tare da wani sharadi ba.
Haka kuma kotun ta umarci hukumar da ta mika wani jami’inta, Ifeanyi Onyewuenyi, ga rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa domin a gudanar da cikakken bincike a kansa.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa ana zargin Ifeanyi Onyewuenyi, da sace Walida, mai shekaru 16 da ke zaune a karamar hukumar Hadejia, jihar Jigawa.
Zargin da ake yi wa jami'in DSS
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa ana zargin Ifeanyi Onyewuenyi, din ne ya sace ta tare da cin zarafinta ta hanyar lalata da ita a shekarar 2023.
Tun daga lokacin da lamarin ya fito fili, ya janyo hankalin jama’a sosai a cikin jihar Jigawa da ma sauran sassan Najeriya.
An kuma ruwaito cewa yarinyar ta haifi ‘ya mace yayin da take hannun jami'in DSS din, Ifeanyi Onyewuenyi.

Source: Original
Wannan lamari ya kara tada kura tare da jawo damuwa kan yadda ake tafiyar da shari’ar, musamman bayan DSS ta ce ta fara bincike da kanta.
Tun a ranar 26 ga Maris, 2026 kotun ta dage yanke hukunci bayan sauraron bangaren masu kara da na masu kare kai, inda daga bisani aka dawo domin yanke hukunci.
Alkali ya caccaki hukumar DSS
Yayin da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai shari’a Hassan Dikko, ya umarci DSS da ta saki yarinyar nan take ba tare da wani sharadi ba.
Haka kuma ya ce dole ne a gabatar da Ifeanyi Onyewuenyi, a mika shi ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike mai zurfi.
Alkalin ya yi Allah-wadai da abin da ya kira kokarin DSS na boye jami’inta da ake zargi da aikata “mummunan laifi.” Ya kuma soke duk wani bincike da DSS ta ce tana yi kan jami’in nata.
A cewarsa, DSS ba ta da ikon shari’a na bincikar jami’inta a irin wannan batu, bisa dokar da ta kafa hukumar tsaro ta kasa.
Ya jaddada cewa ‘yan sanda da kotuna ne kawai ke da hurumin bincike da hukunta irin wadannan laifuka.
Ya ce:
"Halin da DSS ta nuna na boye jami’in da ake zargi da aikata wannan laifi abin Allah-wadai ne.”

Kara karanta wannan
Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House
Lauyan iyalan Walida, Kabiru Adamu, ya yi maraba da hukuncin, yana cewa ya dawo karfin gwiwa ga al’umma kan cewa har yanzu kotu ita ce mafakar talaka.
Kotu ta zauna kan jami'in DSS
A baya, mun wallafa cewa wata kotun Majistare da ke zamanta a Jigawa ta bayar da umarnin cafke wani jami’in SSS kan zargin sace 'ar kankanuwar yarinya a Jigawa.
Ana zargin jami'in mai suna Ifeanyi Onyewuenyi ya tilasta wa wata yarinya mai suna Walida AbdulHadi sauya addini tare da yi mata fyade har ta haifi jaririya.
A zaman kotun, an ba da umarnin kwato yarinyar daga hannun Onyewuenyi, tare da mayar da ita hannun iyayenta gabanin a ci gaba da shari'a a kan lamarin.
Asali: Legit.ng

