Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya

Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta magantu a kan gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya yi game da yuwuwar kai hari Abuja
  • Kakakin yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce sam shi bai da masaniya akan wannan lamari
  • Ofishin jakadancin Amurka dai ya gargadi 'ya'yan kasarsa mazauna Najeriya da su kula sosai kan yuwuwar samun hare-hare

Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata da masaniya kan gargadin da ofishin jakadancin Amurka ya yi a Najeriya game da yuwuwar kai hari babban birnin tarayya Abuja.

Da yake martani ga tambayar da jaridar Leadership tayi masa a jiya Lahadi, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce bai da masaniya kan kowani barazana na tsaro.

Olumuyiwa Adejobi
Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da aka tambaye shi game da shirin yan sanda na dakile harin, kakakin rundunar wanda bai zurfafa magana kan lamarin ba, ya amsa tambayar a takaice da "bani da masaniya".

Kara karanta wannan

Rudani: Amurka da Burtaniya sun ce za kai hare-hare Abuja, sun ba 'ya'yansu dake Najeriya shawari

Hukumar DSS ta bukaci jama'a su kwantar da hankalinsu

Da take martani a nata bangaren, hukumar DSS ta bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu amma dai su zamo masu lura, jaridar Vanguard ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa daga kakakinta, Dr. Peter Afunanya, DSS ta shawarci yan Najeriya da su yi taka-tsantsan, sai dai ta bayar da tabbacin cewa za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya.

Ta bukaci yan Najeriya da su sanar da hukumar bayanai da ke da nasaba da barazana ko ayyukan da basu yarda da shi ba.

US ta gargadi yan kasarta mazauna Najeriya

A ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba ne gwamnatin Amurka ta gargadi 'ya'yan kasarta mazauna Najeriya kan tsaro, inda ta ce akwai yiwuwar samun hare-hare a wuraren taron jama’a a Abuja.

Kara karanta wannan

Tashin hankanli: An gano sansanin horar da 'yan ta'addan IPOB, an kama kasurgumin kwamandansu

Sanarwar ta ce ana iya kai hare-haren ne a kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni da shagunan siyayya, otal, mashawa, gidajen cin abinci da na wasanni har kan jami'an tsaro da sauransu.

Hakazalika ofishin jakadancin Amurkan ya ce zai rage ayyukan yau da kullum saboda gujewa fadawa hadari, rahoton Premium Times.

Yan Sanda Sun Kama Kwamandan IPOB/ESN, Sun Lalata Sansanonin Horar da Tsageru a Ebonyi

A wani labarin, 'Yan sandan jihar Ebonyi sun yi nasarar kame wasu mambobin kungiyar nan ta ta'addanci IPOB da sojojinta ESN bayan wani samamen da ta kai kan wasu sansanonin horar da tsageru.

'Yan sandan sun bayyana cewa, wadannan sansanoni na tsageru suna cikin wani duhun daji ne na kauyen Omege a lardin Agba ta karamar hukumar Ishielu ta jihar, The Cable ta ruwaito.

Chris Anyanwu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya kuma bayyana cewa, jami'ai sun kwato makamai da alburusai da kakin sojoji da dai sauran kayayyakin aikata laifi.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel