Magidanci Ya Gano Cewa Matarsa Tayi Auren Sirri da Wani Maigadi Duk da Suna da ‘Ya’ya 2

Magidanci Ya Gano Cewa Matarsa Tayi Auren Sirri da Wani Maigadi Duk da Suna da ‘Ya’ya 2

  • Zuciyar wani matashi ya karaya bayan ya gano cewa matarsa na da wani mijin da ta boye masa
  • Mijin ya auri motar matarsa don yin yan zirga-zirga lokacin da ya hadu da wani maigadi wanda ya nemi jin dalilinsa na tuka motar matarsa
  • Da yayi masa yan tambayoyi, sai suka gano cewa su din kishiyoyin juna ne domin dai mata daya suke aure su biyun

Wata mata ta sha caccaka a kafofin soshiyal midiya bayan ta auri maza biyu a cikin sirri.

Mazajen biyu basu san da junansu ba har sai da suka ci karo da junansu a hanya sannan suka fara yiwa kansu tambayoyi.

A zahirin gaskiya, motarta ce ta tona mata asiri bayan mijinta na farko ya ari motar don yin wasu yan zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

Hoton mace da namiji da wasu suna zantawa
Magidanci Ya Gano Cewa Matarsa Tayi Auren Sirri da Wani Maigadi Duk da Suna da ‘Ya’ya 2 Hoto: Per Anders, Kupicoo, FG Trade/ Getty images
Asali: Getty Images

Da yake kan hanya, sai wani maigadi ya tunkare shi sannan ya nemi jin dalilinsa na tuka motar matarsa. Ya yi jayayya da maigadin wanda ya gabatar da takardun motar a matsayin shaida.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Don karfafa shaidar, sai maigadin ya fito da hotunan matarsa kuma mace daya ce mai suna Acheing.

Achieng ta tsara yadda take haduwa da mazajen nata biyu. Tana haduwa da daya a karshen mako kawai sannan dayan kuma tana haduwa da shi ne a ranakun aiki.

Mjengoke wanda ya bayar da labarin a Twitter ya ce:

“Ka ari motar matarka don yin wasu zirga-zirga a cikin gari. Da ka ajiye motar sai wani maigadi ya tunkareka sannan cikin mutunci ya tambayeka me kake yi da motar matarsa?
“Sai ka ce masa motar matarka ce. Sai ya kai ka ofishinsa sannan ya nuna maka takardun motar. A halin yanzu, matarka (uwar yaranka 2) ta fada maka cewa ta siya motar ne da bashi da ta dauka a wajen aiki.

Kara karanta wannan

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

“Sai ka fada masa ya nuna maka hoton matarsa. Ya nuna maka hoton matarsa. Dankari! Achieng mataerka ce! Hoto iri daya, hoto iri guda. Ya ce matarsa na aiki a Kericho kuma tana haduwa da shi ne a karshen mako kawai.
“A halin yanzu, matarka na zuwa karbar darasi na digiri na biyu duk karshen mako a jami’ar Masinde Muliro da ke Kakamega, tun shekara daya da ya gabata."

Jama'a sun yi martani

Isaac Adwar ya rubuta:

“Zan koma gida nayi shiru bayan wasu kwanaki na tambayeta ta nuna mun duk bayanan motarta.

Chiso Chris ta ce:

“Lokacin da take da cikin yara biyun, me ta fadawa dayan mutumin ko kuma ta rigada ta haihu kafin ta auri daya mutumin?”

Miss Dee ta ce:

“Na tabbata mijinta ya yi mata wani abu da har ya kai ta ga son samun miji na biyu. Watakila yana yawan musguna mata. Ba za ka ga laifin mace don ta so zaman lafiya ba. Baya ga haka, idan har za ta iya kula da su dukka biyun, bana ganin akwai matsala.”

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

Mace Ba Yar Goyo Bace: Bakano Ya Je Shagalin Auren Aminsa, Ya Gano Budurwarsa Ce Amaryar

A wani labarin, wani matashi dan Najeriya ya shawarci masu amfani da shafukan soshiyal midiya da kada su taba yarda da mace yayin da ya bayyana yadda budurwa tayi rugu-rugu da zuciyar abokinsa.

Sambo Mai Hula ta shafinsa na twitter mai suna @Abdullahiabba_ ya bayyana cewa abokinsa ya halarci shagalin bikin auren wani aminsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.

Ga mamakin abokin Sambo, sai yaga cewa amaryar ba kowa bace face wata budurwa mai suna Fatima wacce ya shafe tsawon shekaru uku suna soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel