Halin Tattalin Arziki Ya Sa NLC Ta Fara Raina Karin Albashin da Tinubu Ya Yi

Halin Tattalin Arziki Ya Sa NLC Ta Fara Raina Karin Albashin da Tinubu Ya Yi

  • Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ko da ma’aikata za su rika karbar albashin Naira miliyan daya, hakan ba zai amfane su ba
  • Ajaero ya jaddada cewa hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa sun riga sun cinye karfin ikon sayayya na ma’aikata a Najeriya
  • Game da sabon mafi karancin albashi, shugaban NLC ya ce tattaunawa za ta gudana ne bisa ka’idojin doka, kuma ba za a gaggauta yin ta ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, ya yi magana game da tasirin tattalin arziki da mafi karancin albashin da ake biyan ma'aikata a Najeriya.

Joe Ajaero ya bayyana cewa babban abin da kungiyar ke damun ta a halin yanzu shi ne yadda darajar Naira ke faduwa, ba wai kawai adadin albashin da ake biya ba.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Daga kwanciya barci, an tarar da gawar fitaccen jarumin fim a Najeriya

NLC ta yi magana game da halin da tattalin arziki yake ciki wanda ya rusa karfin mafi karancin albashi.
Shugaban NLB, Joe Ajaero ya jagoranci 'yan kwadago a zanga-zaga kan albashi a Abuja. Hoto: @NLCHeadquarters
Source: Twitter

Tasirin tattalin arziki ga albashin ma'aikata

A wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata a Abuja, Ajaero ya ce tsadar rayuwa ta sanya rayuwar ma’aikata cikin garari.

Dangane da darajar kudin kasar, Ajaero ya bayyana cewa:

“Ko da ma’aikatan Najeriya za su rika karbar Naira miliyan daya, hakan ba zai yi ma’ana ba muddin Nairar ba ta da daraja. Abin da muke nema shi ne kudin da zai iya rike ma’aikaci da iyalinsa a kalla har zuwa karshen wata.”

A cewar shugaban NLC, karuwar hauhawar farashin kayayyaki ya jefa ma'aikata a tsaka mai wuya, inda suke kasa yin abubuwa da suka hada da biyan kudin sufuri, abinci da gidan haya.

Tattaunawa kan sabon albashi

Ajaero ya tabo batun sabon mafi karancin albashi na kasa, inda ya bayyana cewa wannan tsari ne da doka ta tanada kuma dole ne a bi matakan da suka dace.

Kara karanta wannan

Yana ajiye mukamin minista, Tuggar ya fadi abin da ya jawo ta'addanci a Bauchi

Ya bayyana cewa kungiyar kwadago za ta fara tattaunawa ne a lokacin da ya dace kafin karewar wa’adin albashin da ake kai yanzu, inda ya jaddada cewa ba za su bari a gaggauta yin hakan ba domin muradun zabe.

Shugaban NLC ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda karin farashin man fetur ya kara jefa ma’aikata cikin kuncin rayuwa, wanda hakan ya shafi farashin sufuri da na abinci.

NLC ta ce za ta dago da batun sabon albashi idan lokacin hakan ya yi.
Shugaba Bola Tinubu na sanya hannu kan takardu (hagu) da Joe Ajaero yana magana a madadin NLC a taron ranar ma'aikata. Hoto: @officialABAT, @NLCHeadquarters
Source: Facebook

Rikicin kungiyoyin fansho

Ya bukaci gwamnati da ta samar da tsauraran manufofi kan makamashi domin rage dogaro da sauye-sauyen da ke faruwa a kasashen duniya, in ji rahoton Punch.

Baya ga batun albashi, Ajaero ya koka kan yadda ake samun rarrabuwar kawuna da yawaitar kungiyoyin fansho, wanda ya ce hakan yana haifar da rudani a cikin tsarin.

Ya bayyana cewa tuni NLC ta rubuta wasika ga masu ruwa da tsaki domin kiran taro don daidaita al’amura da tabbatar da cewa ana gudanar da sha’anin fansho cikin hadin kai.

Ana neman kara wa ma'aikata albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta fara sabuwar fafutukar nemawa ma'aikatan Najeriya karin albashi daga gwamnati.

Kara karanta wannan

Matakan da gwamnati ta dauka da aka samu bullar annobar COVID 19 a Najeriya

'Yan kwadago sun bayyana cewa ma'aikata na shan wahala sosai duk da karin mafi karancin albashi da aka yi zuwa N70,000 a baya.

Kungiyoyin kwadago da suka nemi karin albashin sun nemi zama da ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya domin samun mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com