Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Ayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC Na Wata Jiha a 2023

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Ayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC Na Wata Jiha a 2023

  • Kotu ta yanke hukunci kan wanda yake halastaccen dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Cross River
  • Mai shari'a Justis Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya da ke Calabar ta ce Bassey Otu ne dan takarar gwamna na APC a zaben 2023 mai zuwa
  • Owan Enoh ya garzaya kotu bayan kammala zaben fidda gwanin jam'iyyar mai mulki a watan Mayu inda ya kalulanci nasarar Otu

Cross River - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Calabar ta ayyana Bassey Otu a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Cross River.

Justis Ijeoma Ojukwu ce ta ayyana haka yayin da take zartar da hukunci a kan wata kara da aka shigar a gabanta, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

Logon APC
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Ayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC Na Wata Jiha a 2023 Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: UGC

Bayan zaben fidda gwanin APC a watan Mayu, Owan Enoh wanda yana daya daga cikin wadanda suka nemi takarar tikitin gwamna na jam’iyyar mai mulki a jihar ya garzaya kotu.

Enoh ya kalubalanci Otu sannan ya nemi kotu ta yi watsi da shi a matsayin dan takarar gwamna na APC a babban zaben 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da take zartar da hukunci, Ojukwu ta ce:

“Cewa dole wani dan takara da ke neman kujerar gwamna ya kasance dan Najeriya, ya cika ka’idar shekarun da ake bukata da kuma muhimman abubuwa a bisa kundin tsarin mulki.”

Ta ce yancin jam’iyyar siyasa ce ta fitar da wanda take so ya zama dan takararta na gwamna.

Wannan hukunci ya kawo karshen rade-radi da rabuwar kan da jam’iyyar APC reshen Cross River ke fama da ita yayin da jam’iyyar ke shirin fara kamfen din 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Kiristocin APC a Arewa Sun Yi kira Ga Kauracewa Kamfen Din 2023 Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

A wani labarin, mun ji cewa yayin da aka kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, wasu kiristoci a jam’iyyar sun yi kira ga kauracewa jam’iyyar mai mulki a zaben 2023, rahoton Vanguard.

A lokacin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba, kiristocin sun jadadda matsayinsu na kin amincewa da tikitin Musulmi da Musulmi na APC.

Kiristocin karkashin jagorancin babban sakataren kungiyarsu, Lukas Bako, sun ce lallai sai APC ta ajiye hadin da tayi na Bola Tinubu da Kashim Shettima kafin ta samu goyon bayan kiristoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel