Uba Ya Gaji Da Lamarin Diyarsa Da Ta Ishe Shi Da Kuka Yayin da Yake Aikin Rainonta, Ya Taya Ta a Bidiyo
- Wani bidiyon TikTok ya nuno yadda wani uba yi yiwa karamar diyarsa da ke kuka dabara har ta yi shiru
- Mahaifiyar yarinyar ta yi nisan kiwo inda ta bar masa aikin raino, sai dai jinjirar ta bare baki tana ta kuka sai kawai shima ya taya ta.
- Ganin mahaifin nata na kuka sai kyakkyawar yarinyar tayi shiru tana kallonsa cike da mamaki
Masu amfani da TikTok na ta tofa albarkacin bakunansu ganin bidiyon wani uba da ya taya karamar diyarsa kuka yayin da yake aikin raino.
Kyakkyawar yarinyar na ta ihu kuma hakan ya kular da mutumin inda ya rasa abun yi don hana ta kuka. Wellington Roberts ne ya wallafa bidiyon.
Mahaifiyar yarinyar ta yi nisan kiwo kuma ga dukkan alamu yarinyar na neman uwar tata ne don jin duminta.
Don lallashin yarinyar, sai mutumin ya fashe da kuka shima yana kokwayon muryar yarinyar cikin siga mai ban dariya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yarinyar na jin muryar mahaifinta yana kuka sai ta yi shiru tana kallonsa cike da mamaki.
Wannan dabara tasa tayi aiki sosai inda mutumin ya bayyana cewa kukan jin dadi kawai yarinyar ke yi.
Wannan fasahar raino na mutumin ya burge masu amfani da TikTok.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
@Marvelous ta yi martani:
“Yarinyar ma ta shiga rudani.”
@Alyssa ta ce:
“Tana kallo kamar yallabai wannan fasahata ce ba taka ba.”
@Yvonne001 ta ce:
“A ranta tana cewa wani irin uba ne wannan?”
@onyinjubilee ta yi martani:
“Kukan yaro akwai dadi duk mai neman haihuwa Allah yasa ku ji kukan jinjiri a gidanku badi war haka mutane za su taya ku murna.”
Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo
A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.
Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.
Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.
Asali: Legit.ng