Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa

Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa

  • Nehemiah Dalung, dan tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya kwanta dama
  • Marigayin mai shekaru 33 ya mutu a safiyar yau Litinin, 24 ga watan Oktoba, bayan ya yi fama da rashin lafiya
  • Da yake sanar da babban rashin nasa, Dalung ya ce ba za su taba mantawa da rayuwar da marigayin yayi da su ba, inda ya fawwala lamarin ga Ubangiji

Allah ya yiwa dan tsohon ministan wasanni Solomon Dalung, Nehemiah Dalung, rasuwa yana da shekaru 33 a duniya.

Nehemiah ya mutu ne a safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, bayan ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya .

Solomon Dalung
Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa Hoto: Punch
Asali: UGC

Mahaifinsa, Dalung ne ya sanar da labarin mutuwar tasa a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook yana mai tawali’u ga ubangiji.

Ya rubuta a shafin nasa:

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Fito Ta Fadawa Kotu Asalin Dalilin Cigaba da Tsare Nnamadi Kanu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk da cewar rayuwar Nehemiah ta zo karshe kafin mu shirya mata, ba za mu taba mantawa da rayuwar da yayi da mu ba.
“Shekarun Nehemiah Dalung 33. Dana ne shi.
“Babu wata kalma da za ta nuna irin radadi da bakin cikin rasa da a yayin da yake ganiyar samartaka, amma mun fawwalawa Allah mai bayarwa da karba.
“Allah ya ji kansa.”

Jama’a sun mika ta’aziyyarsu

IG Wala ya ce:

“Wannan labari ne mara dadi a garemu kuma babban rashi a garemu. Allah Ya bada hakuri da wannan rashin. Allah ya ji kansa da rahama.”

Fadima Ibrahim • ta rubuta:

“Lallai wannan abu akwai ciwo .”

Kelechi Deca ya ce:

“Ina mai mika ta’aziyyata.”

Amb Innocent Nduanya ya ce:

“Ina mai mika ta’aziyyata yallabai.”

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Na Yarda Na Amsa Lambar Girman da Shugaban kasa Ya Ba Ni – Fasto

Kakakin Majalisar Dokokin Jiha a Najeriya Ya Rasu

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa kakakin majalisar dokokin jihar Ekiti, Hon Funminiyi Afuye ya rasu yana da shekaru 66 a duniya, jaridar The Nation ta rahoto.

Afuye wanda ke wakiltan mazabar Ikere 1 ya rasu ne a yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa wani dan majalisa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce marigayin ya kamu da rashin lafiya inda aka kwashe shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ekiti da ke Ado-Ekiti a safiyar yau Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel