Sanata Ta Fasa Kwai, Ta Fadi yadda Aka Canja Wasu Bangarori a Sabuwar Dokar Zabe
- Sanatar Abuja, Ireti Kingibe, ta bayyana fargabar cewa an canja wasu sassa na Dokar Zaɓe ta 2026 bayan majalisa ta miƙa wa shugaban ƙasa
- Ireti Kingibe ta yi zargin cewa an cire ko an raunana matakan tsaro da aka saba gani a jikin takardun ƙuri'a na INEC, wanda zai bude kofar tafka maguɗi
- Wannan kalami na 'yar majalisar dattawan ya yi daidai da koke-koken Mike Igini, tsohon kwamishinan INEC, wanda ya nuna damuwa kan sashe na 63
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Sanata Ireti Kingibe ta tada kura game da sabuwar dokar zaɓe ta 2026 da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026.
Sanatar ta yi zargin cewa an "jirkita" wasu sassa na dokar yadda ba su yi daidai da sakamakon tattaunawar da aka yi da masu ruwa da tsaki ba a lokacin gyaran dokar.

Source: Facebook
Sanata Ireti Kingibe ta magantu kan dokar zabe
Yayin da take jawabi a wani shirin gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, Kingibe wadda ke cikin kwamitin gyaran dokar zaɓe ta ce:
"Waɗannan sauye-sauyen ba sa cikin ainihin takardunmu na farko. Na gaya wa wani cewa zan iya nuna masa takardar da nake da ita domin ya gani da idonsa."
Babban abin da ya fi tayar wa Sanata Kingibe hankali shi ne raunana matakan tsaro a kan takardun ƙuri'a na hukumar INEC.
Ta yi gargaɗin cewa hakan babban haɗari ne ga sahihancin zaɓe a Najeriya, duba da cewa a baya ana amfani da takardu masu lambobin tsaro na musamman domin kauce wa yin jabun ƙuri'u.
"A wane zaɓe ne aka taɓa yi inda takardun ƙuri'a na INEC ba su da matakan tsaro, har ta kai ga za ka iya kawo kowace irin takarda ka yi zaɓe da ita? Wannan bai taɓa faruwa ba." — Sanata Ireti Kingibe.
'Babu wani sauyi sosai a dokar zabe' - Bincike
Wannan kalami nata ya yi daidai da koke-koken Mike Igini, tsohon kwamishinan INEC, wanda ya bayyana cewa Sashe na 63 na dokar yana ba jami’an zaɓe ikon karɓar takardun da ba su da tambarin hukumar idan har sun gamsu da asalinsu.
Duk da koke-koken Sanata Kingibe, binciken da jaridar TheCable ta gudanar ya nuna cewa Sashe na 63 na dokar, wanda shi ne ake tattaunawa a kai, kusan ɗaya yake da yadda yake a dokar 2022.
Dokar ta bayyana cewa duk takardar ƙuri'a da ba ta da tambarin hukuma ba za a ƙirga da ita ba, sai dai idan jami'in zaɓe ko mai lura da zaɓe ya gamsu cewa takardar ta fito ne daga littafin da hukumar ta bayar zuwa mazaɓa.

Source: Twitter
Banbancin dokar zaben 2022 da ta 2026
Binciken ya nuna cewa sauyin da aka samu a shekarar 2026 kaɗan ne wanda ya shafi harshen turanci inda aka sauya kalmar "idan" zuwa "inda".

Kara karanta wannan
Amurka za ta jefa Iran a sabuwar matsala, fada ya koma kan gasar cin kofin duniya
To sai dai kalaman Sanata Kingibe sun nuna cewa tana da wasu bayanai na daban game da faffadan sauye-sauye a cikin kunshin garambawul ɗin da aka gabatar wa shugaban ƙasa.
Tana ganin cewa wannan canji na iya shafar yadda za a gudanar da zaɓukan da ke tafe a ƙasar cikin gaskiya da adalci.
Tinubu ya sanya hannu kan dokar zaben 2026
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta shekarar 2026 a fadar gwamnati dake Abuja a ranar 18 ga Fabrairu, 2026.
Tinubu ya bayyana cewa akwai bukatar yin amfani da tsarin hannu wajen tura sakamakon zabe domin kaucewa matsalar yanar gizo.
Shugaban ya sanya wa kudirin hannu ne bayan an kai ruwa rana a Majalisar dattawa, musamman turjiyar 'yan hamayya a majalisa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

