Kiristocin APC a Arewa Sun Yi kira Ga Kauracewa Kamfen Din 2023 Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

Kiristocin APC a Arewa Sun Yi kira Ga Kauracewa Kamfen Din 2023 Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

  • Mambobin kungiyar kiristocin APC a Arewa sun yi kira da a gaggauta sauya Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu
  • Kiristocin arewan sun bayyana kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a matsayin shirme kawai
  • A cewar Kiristocin, ya zama dole APC ta gane cewa su din manyan masu fada aji ne a cikin jam’iyyar

Abuja - Yayin da aka kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, wasu kiristoci a jam’iyyar sun yi kira ga kauracewa jam’iyyar mai mulki a zaben 2023, rahoton Vanguard.

A lokacin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja a ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba, kiristocin sun jadadda matsayinsu na kin amincewa da tikitin Musulmi da Musulmi na APC.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Sha Alwashin Yi wa Tinubu Gagarumin Kamfen

Shettima da Tinubu
Kiristocin APC a Arewa Sun Yi kira Ga Kauracewa Kamfen Din 2023 Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi Hoto: APC Vanguard
Asali: Twitter

Kiristocin karkashin jagorancin babban sakataren kungiyarsu, Lukas Bako, sun ce lallai sai APC ta ajiye hadin da tayi na Bola Tinubu da Kashim Shettima kafin ta samu goyon bayan kiristoci.

Bako ya bayyana bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar da aka yi kwanan nan a matsayin shirme yayin da ya bayyana cewa APC bata da kwakkwaran dama a zaben shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa a karkashin wannan tsari da ke kasa, Kiristoci za su dandana kudarsu karkashin gwamnatin APC a Najeriya.

Bako ya kara da cewar kiristocin arewa na tare da matsayin kungiyar kiristocin Najeriya.

Ya ce:

“Kiristocin da ke cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC maciya amana ne wadanda suka siyar da kansu saboda abun duniya.”

Don haka, kungiyar ta yi kira ga shugabancin APC da tayi abun da ya dace na maye gurbin Shettima da dan takara kirista kafin a fara kamfen.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

Saboda haka sun shawarci kiristoci a APC da su yi murabus cikin mutunci don zanga-zanga har sai an yi abun da ya dace.

Ya kuma bayyana cewa kungiyar kiristocin APC ta damu da cewar rashin mutunta kiristoci a arewacin Najeriya da shugabancin APC ke yi ya kai intaha, wanda yunkuri ne na rage kiristoci a arewacin Najeriya da gangan.

Da suke bayar da shawararsu, kungiyar ta yi kira ga a gaggauta maye gurbin Shettima a matsayin abokin takarar Bola Tinubu, rahoton Sahara Reporters.

Tinubu Ya Bayyana Yan Takara Biyu Da Zasu Ba Shi Wahala a 2023, Ya Watsar da Kwankwaso

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa karƙaahin inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya tsayar da fafatawar zaɓen shugaban kasa a 2023 a tsakanin mutum uku kacal.

Jumullar jam'iyyun siyasa 18 ne suka tsayar da masu neman kujera lamba ɗaya a Najeriya, amma ɗan takarar jam'iyya mai mulki ya nuna cewa shi da 'yan takara biyu ne zasu gwabza a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari ya kaddamar da kwamitin da zai tallata Tinubu a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a kalaman Tinubu ya nuna cewa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party ne kaɗai zasu fafata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel