Tsohon Sufeta Janar Ya Zargi APC da Neman Hana Shi Takarar Gwamna

Tsohon Sufeta Janar Ya Zargi APC da Neman Hana Shi Takarar Gwamna

  • Tsohon sufeto janar na ‘yan sanda Mohammed Adamu Abubakar ya yi magana kan yanayin siyasar jihar Nasarawa a yanzu
  • Mohammed Adamu ya zargi shugabannin APC da shirin matsa wa shugabannin gundumomi su mara wa ɗan takarar da gwamna ya fi so baya
  • Ya bayyana cewa wannan tsari wata dabara ce ta siyasa domin karkatar da zaɓen fitar da gwani, yana mai gargadi kan hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Tsohon sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu Abubakar, ya zargi shugabannin jam’iyyar kan fitar da dan takara.

Tsohon dan sandan wanda kuma yana daga cikin masu neman takarar gwamnan Nasarawa ya ce ana shirin karkatar da zaɓen fitar da gwani mai zuwa.

Tsohon shugaban yan sanda ya zargi APC da son kai
Gwamna Abdullahi Sule da tsohon sufeta-janar na yan sanda, Mohammed Adamu Abubakar. Hoto: Dalhat Usman, Gov. Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Ana zargin APC da karfa-karfa a Nasarawa

Ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban kwamitin wayar da kai da shirye-shirye na kamfen dinsa, Isah Nathaniel, a Lafia, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Peter Obi ya bayyana dalilin ganawa da Jonathan

Mohammed Adamu ya ce ana matsa wa shugabannin gundumomi a dukkan gundumomi 147 su mara wa ɗan takarar da gwamna ya fi so baya.

Ya ce:

“A bayyane yake, wannan ba tsarin jam’iyya ba ne; wannan dabara ce ta siyasa mafi muni. Abin da ake ɓoye da sunan tsari, a zahiri yunƙuri ne na kwace muradin mambobin jam’iyya da tilasta sakamakon da aka riga aka tsara.”

Zargin ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan shugaban jam’iyyar a jihar, Aliyu Bello, ya yi alƙawarin samar da adalci ga dukkan ‘yan takara a zaɓen fitar da gwani.

Nuna magajin Gwamna Sule a Nasarawa ya bar baya da kura
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Hoto: Gov. Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Gargadin da tsohon sufeta-janar ya yi

Tsohon IGP ɗin ya gargadi cewa amfani da shugabannin gundumomi don wata manufa ta ɓoye na iya jefa jam’iyyar cikin rikici tare da rage ƙarfinta kafin zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki suka amince da amfani da tsarin zaɓen kai tsaye ga dukkan muƙaman zaɓe.

Saboda haka, ya buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta lura da wannan lamari tare da ɗaukar mataki domin kare martabar jam’iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

Gobara ta lalata dukiyar miliyoyin Naira a gidan Sarki a Abuja

Haka kuma ya roƙi kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar da ya shiga tsakani cikin gaggawa domin dakatar da wannan “sabawa doka da ke ƙara bayyana” tare da dawo da tsarin doka, cewar Daily Post.

Sai dai a nata ɓangaren, jam’iyyar ta ce za ta tabbatar da gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani ba tare da nuna bambanci ba.

Shugaban jam’iyyar, Aliyu Bello, ya ce ba su ƙoƙarin cutar da kowa, yana mai cewa gwamna Sule na da ‘yancin goyon bayan duk wanda ya ga ya dace, ba tare da hana sauran ‘yan takara fafatawa ba.

Farfesa ya sha alwashi kan takarar gwamna

Mun ba ku labarin cewa Farfesa Mohammed Sani Haruna ya bayyana matsayarsa kan takarar Gwamnan Nasarawa bayan gwamna ya nuna magajinsa.

Farfesan ya ce ba zai janye takararsa ba duk da goyon bayan Gwamna Sule Abdullahi ga Sanata Ahmed Aliyu Wadada.

Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a Keffi, inda ya ce shawarar su ce za ta jagoranci matakin da zai dauka kan takararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.