2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

  • Jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas za ta kaddamar da motoci da kwamitin yakin neman zabenta a yau Litinin, 24 ga watan Oktoba
  • Babu hoton dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, a jikin motocin da aka kawata domin gudanar da kamfen din na zaben 2023
  • Alaka dai ta yi tsami tsakanin Atiku da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda ya nace sai dai Ayu ya sauka daga mukamin shugaban jam’iyyar

Rivers - Ko sama ko kasa ba a ga hoton dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba a jikin motocin kamfen din jam'iyyar na 2023 a jihar Ribas.

Za a kaddamar da motoci kimanin guda 25 da aka kawata da hotunan yan takarar jam'iyyar adawar a ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba 2022.

Hakazalika za a kaddamar da sakatariyar yakin neman zaben jam'iyyar wanda ke a hanyar Woji da ke GRA, Port Harcourt, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

PDP a Jihar Plateau Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023

Motocin kamfen din PDP a Ribas
2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar Hoto: Leadership
Asali: UGC

Kwamitin yakin neman zaben na kunshe da tsohon shugaban PDP a jihar, Cif Felix Obuah, a matsayin darakta janar yayin da Gwamna Nyesom Ezenwo Wike ke rike da mukamin shugaba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnonin PDP biyar sun nemi a maye gurbin Ayu da wani a matsayin sharadin marawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar baya, a zaben 2023.

Sai dai kuma, da yake zantawa da jaridar Leadership, tsohon dan majalisa, Cif Ogbonna Nwuke, ya ce 'kawata motocin da aka yi da kalolin PDP ya tabbatar da kasancewar Wike da sauran gwamnonin hudu 'ya'yan jam'iyyar.

Nwuke ya ce:

"Ban ga motocin da idanuna ba. Zan samu damar tabbatar da hakan idan ofishin kamfen din ya bude kofarsa ga jama'a a ranar Litinin. Idan kamar yadda ka fadi motocin basa dauke da hotunan Atiku, kada hakan ya zama abun mamaki.

Kara karanta wannan

2023: Gangamin Taron Kamfen PDP a Edo Ya Sake Fito da Rikicin Jam'iyyar, Atiku Ya Shiga Matsala

"Gwamnonin PDP biyar wato G5 sun sha alwashin ci gaba da kasancewa a PDP. Kasancewar an kawata motocin da kalolin PDP ya tabbatar da su din 'ya'yan jam'iyya ne.
"Yana rubuce cewa gwamnonin G5 sun janye daga kwamitin yakin neman zaben Atiku. Idan kamar yadda ka fadi motoci basa dsuke da fuskar Atiku, hakan na nufin cewa gwamnonin sun tsaya kan bakarsu na kin yiwa Atiku kamfen idan ya ki sauraron bukatunsu a PDP."

PDP a Jihar Arewa Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023

A wani labarin, Jam’iyyar PDP a Plateau ta yi alkawarin kawowa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, kuri’u miliyan biyu a 2023 da kuma lashe duk wasu mukaman siyasa a jihar.

Jiga-jigan jam’iyyar a jihar sun bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar, rahoton AIT.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari ya kaddamar da kwamitin da zai tallata Tinubu a Najeriya

Dandazon magoya bayan jam'iyyar sun halarci bikin kaddamar da kwamitin kamfen din na Atiku-Mutfwang gabbanin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel