'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Addini a Taron Wa'azi, Sun Sace Mutane Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Addini a Taron Wa'azi, Sun Sace Mutane Masu Yawa

  • 'Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Ilejemeje a jihar Ekiti, inda suka kashe fasto tare da sace masu bauta da dama ana taron wa'azi
  • Lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Talata yayin da ake gudanar da taron wa’azin addinin Kirista a Eda Oniyo
  • Shugaban karamar hukumar Ilejemeje, Pius Alaba, ya tabbatar da lamarin, kuma ya yi karin bayani game da faston da aka kashe a harin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ekiti – Tashin hankali ya mamaye al'ummar Eda Oniyo a jihar Ekiti bayan da wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hari kan taron addini, inda suka kashe wani fasto, suka sace mutane da dama.

Maharan sun mamaye filin taron ne a lokacin da ake tsaka da gudanar da wa’azi, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jefa masu bautar cikin firgici.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka malamin addini da iyalansa a Plateau

'Yan bindiga sun kashe fasto tare da sace masu ibada a Ekiti
Kiristoci na gudanar da ibada a cocin Cherubim and Seraphim. Hoto: @SeraphStories
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kashe malamin addini

Wani jagoran al'umma a yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun zo ne a ayari kuma suna dauke da muggan makamai, in ji rahoton The Guardian.

A cewarsa:

“'Yan bindiga sun farmaki mutane lokacin da ake taron wa'azin coci a garin Eda Oniyo. Sun harbe fasto, sannan sun sace masu ibada da dama, ciki har da dattawa da yara, suka tafi da su daji."

Ya kara da cewa har yanzu iyalai da dama na ci gaba da neman danginsu da suka bata a yayin harin, wanda hakan ya bar yankin cikin matsanancin firgici.

Yawan mutanen da aka sace

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar da takamaiman adadin mutanen da maharan suka tafi da su cikin daji ba.

Shugaban karamar hukumar Ilejemeje, Pius Alaba, ya bayyana cewa rahotanni daga makarantar da taron ya gudana sun nuna cewa mutane kusan 50 ne suka halarci wa'azin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan bayin Allah a Katsina, an samu asarar rayuka

Alaba ya tabbatar da cewa an riga an kai gawar faston da aka kashe zuwa dakin ajiyar gawa, kamar yadda rahoton Premium Times ya nuna.

Ya kara da cewa hukumomin yankin na kokarin tantance yawan mutanen da suka rage a hannun maharan domin sanin matakin da za a dauka na gaba.

'Yan bindiga sun sace masu ibada tare da sace masu ibada a taron coci.
Taswirar jihar Ekiti, inda 'yan bindiga suka kashe fasto da masu ibada. Hoto: Legit.ng
Source: Facebook

Karuwar hare-hare kan masu ibada

Duk wani kokari na jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ya ci tura. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Sunday Abutu, bai amsa kiran waya ko sakonnin da aka tura masa ba.

Wannan hari ya kara fito da kalubalen tsaro da ke damun yankunan karkara a sassan kasar nan, musamman hare-haren da ake kai wa wuraren bauta da taron jama'a.

Mazauna garin Eda Oniyo na kira ga gwamnati da ta gaggauta tura jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sace da kuma kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

An kashe fasto da iyalansa a Filato

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci wanda ya jawo asarar rayuka a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Yana ajiye mukamin minista, Tuggar ya fadi abin da ya jawo ta'addanci a Bauchi

Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wani fasto tare da wasu daga cikin iyalansa a yayin harin da suka kai cikin dare.

Lamarin ya kara sanya tsoro a zukatan mazauna yankunan da aka kai harin, inda wasu daga cikinsu suka bar kwana a gidajensu don tsira da rayukansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com