Tsaro: Kasar Jamus Ta Shigo Najeriya, Ta Shiga Kauyukan da aka kai Hare Hare
- Wani wakilin gwamnatin kasar Jamus ya shiga wasu kauyukan Najeriya domin duba wadanda aka kai wa hare-haren a baya-bayan nan
- Thomas Rachel ya shiga wasu yankunan jihar Benue tare da alkawarin cewa suna shirye wajen tallafawa Najeriya ta magance rashin tsaro
- Gwamnatin jihar Benue ta yaba wa Thomas Rachel bisa zuwa wuraren da aka kai hari tare da cewa tana shirye domin daukar mataki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Mazauna yankin Yelwata a Jihar Benue sun yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin kare su da kuma ba su tallafin jin kai.
A lokaci guda, kasar Jamus ta sake jaddada kudirinta na taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar rashin tsaro da kuma inganta zaman lafiya tsakanin al’umma.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa kwamishinan gwamnatin Jamus kan ‘yancin addini, Thomas Rachel, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata bayan zuwa Benue.
Bayanin wakilan Jamus kan tsaron Najeriya
Rachel, wanda ya ce ziyararsa zuwa Yelwata ta matukar taba shi, ya bayyana cewa wadanda suka tsira daga harin da aka kai a watan Yuni 2025 sun nuna damuwa kan tsaronsu da makomarsu.
“Har yanzu ina cikin damuwa kan abin da na gani a ziyarata zuwa Yelwata, inda aka yi kisan gilla a watan Yuni 2025. Sama da Kiristoci 200 aka kashe a wurin.
“Mutanen da na gana da su sun nemi tsaro. Sun tambayi abin da gwamnati za ta iya yi. Sun nemi tallafi, kuma suna son a ba su damar komawa gidajensu na asali daga sansanonin ‘yan gudun hijira,”
In ji shi.
Rachel ya ce rashin tsaro na ci gaba da zama babbar matsala a fadin kasar, yana mai jaddada cewa Kiristoci da Musulmi duk suna fuskantar barazanar ‘yan ta’adda.
“Za ka ga cewa Kiristoci da Musulmi suna da cikin matsala, makiyin su daya ne — wato ‘yan ta’adda. Don haka na bayyana cikakken goyon bayana ga Najeriya,”
In ji shi.

Source: Original
Martanin jihar Benue ga Jamus
A nasa bangaren, gwamnan jihar, ta bakin mataimakinsa Barrista Dakta Sam Ode, ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da adalci da kuma karfafa hanyoyin samar da zaman lafiya.
Ya ce hijirar makiyaya daga kasashen yammacin Afirka a lokutan damina ta kara tsananta rikice-rikicen da ke tsakanin makiyaya da manoma, sakamakon karuwar matsin lamba kan filaye da wuraren kiwo.
Hadimin mataimakin gwamnan, Ior Ikyereve ya wallafa a Facebook cewa gwamnatin jihar ta ce kasancewar manoma ne mafi yawan mutanen Benue na kara jawo rikici da makiyaya.
Jamus ta caccaki shugaba Donald Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya caccaki shugaban Amurka, Donald Trump kan yakin Iran.
Merz ya bayyana cewa Amurka ta shiga yaki da Iran ba tare da wani shiri ba, kuma Tehran ta ba Donald Trump kunya a idon duniya.
Ya kuma tabbatar da cewa yakin ya shafi tattaln arzikin Jamus tare da cewa suna duba matakan da ya kamata a dauka kan Hormuz.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

