Matashi Ya Gwangwaje Matar Da Ke Bashi Abinci Kyauta Lokacin Da Bai Da Ko Kwabo, Ya Mallaka Mata Gida

Matashi Ya Gwangwaje Matar Da Ke Bashi Abinci Kyauta Lokacin Da Bai Da Ko Kwabo, Ya Mallaka Mata Gida

  • Wani matashi ya ba da labarin yadda abubuwa suka sauya a rayuwar wata mai siyar da abinci da ke kyautatawa wani kwastamanta
  • Kwastaman ya shafe tsawon lokaci yana karbar abinci kyauta daga wajen mai siyar da abincin har Allah ya buda masa
  • Bayan ya samu aiki mai kyau, sai mutumin ya tuna da wannan mai abinci sannan ya siya mata dankareren gida don nuna godiya

Wata mai sana’ar siyar da abinci ta tsinci dami a kala inda ta mallaki gida nata na kanta bayan kyautatawar da ta yiwa wani matashi.

Matar wacce ke da kirki sosai ta dade tana baiwa matashin abinci kyauta sannan wasu lokutan ta siyar mai da abinci bashi.

Mai abinci
Matashi Ya Gwangwaje Matar Da Ke Bashi Abinci Kyauta Lokacin Da Bai Da Ko Kwabo, Ya Mallaka Mata Gida Hoto: @dexterouz11, agafapaperiapunta, Jonathan Knowles/Getty images
Asali: Getty Images

Matashin ya fara shakku inda ya nemi jin dalilinta na kyautata masa, inda a karshe matar ta bude baki ta fadi dalilinta na aikata hakan.

Kara karanta wannan

Magidanci Ya Gano Cewa Matarsa Tayi Auren Sirri da Wani Maigadi Duk da Suna da ‘Ya’ya 2

Mai siyar da abincin ta magantu

Mai sana’ar abincin ta ce tana yi masa kallon mutum da zai yi nasara sosai nan gaba a rayuwa kuma tana son kasancewa cikin wadanda suka tallafa masa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba a jima da yin haka ba, sai mutumin ya samu babban aiki sannan ya mallakawa matar da ke kyautata masa gida.

Goodnewsbringer wanda ya wallafa labarin a Twitter ya ce:

“Makwabcina ya bani labarin wannan matar da ke da gidan abinci wacce ke basa bashin abinci na tsawon watanni. Daga baya sai ta fara bashi abinci kyauta. Ya zargi hakan sai ya fadama abokansa. Abokansa sun ce watakila matar na sonsa ne. daga baya sai ya hadu da matar sannan ta fada masa cewa tana kallon shi a matsayin wanda zai yi nasara a rayuwa. Yanzu yana aiki a wani babban kamfani kuma ya baiwa matar gida.”

Kara karanta wannan

Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

Kalli wallafar a kasa:

Da Legit.ng ta tuntubi Dexterouz11, ya tabbatar da cewar siyan gidan aka yi ba haya aka kama ba.

Ya kuma bayyana cewa gidan na nan a jihar Lagas, Najeriya.

Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

A wani labari na daban, wani mutumin kasar Malawi mai suna Francis Banda wanda ke zaune a yankin Ntcheu ya hau kanen labarai bayan ya rushe gidaje biyu a kokarinsa na daukar fansar yaudararsa da aka yi.

Malawi 24 ta rahoto cewa matar Banda ta rabu da shi kwanan nan don kasancewa da wani daban, lamarin da ya kona masa rai har ya kai ga ruguza gidajen da ya gina mata da surukarsa.

A bisa ga wani faifan murya da ya saki, ya bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru 13 da matarsa kuma har sun haifi yara uku.

Kara karanta wannan

Hotunan Diyar Jackie Chan Tana Rayuwa Cikin Fatara a Canada Sun Bayyana

Asali: Legit.ng

Online view pixel