Hotuna: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi a Wajen Bude Taron Lafiya Na Duniya Da Ke Gudana a Koriya Ta Kudu

Hotuna: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi a Wajen Bude Taron Lafiya Na Duniya Da Ke Gudana a Koriya Ta Kudu

  • Shugaban kasa Buhari ya halarci bude taron lafiya na duniya da ke gudana a kasar Koriya ta Kudu
  • Shugaban Najeriyan ya yi jawabi a wajen taron wanda ake yi a birnin Seoul a yau Talata, 25 ga watan Oktoba
  • Wannan shine karo na farko da kungiyar lafiya ta duniya da gwamnatin Koriya ke shirya irin wannan taro

Koriya ta Kudu - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi a wajen bude taron harkokin lafiya na duniya da ke gudana a birnin Seoul, kasar Koriya ta Kudu.

Ana gudanar da taron mai taken ‘World Bio Summit’ ne a yau Talata, 25 ga watan Oktoba.

Shugaba Buhari
Hotuna: Shugaba Buhari Ya Yi Jawabi a Wajen Bude Taron Lafiya Na Duniya Da Ke Gudana a Koriya Ta Kudu Hoto: @Buharisallau1
Asali: Facebook

Hadimin shugaba Buhari kan harkokin sadarwan zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Kamar yadda muka bayyana a baya, wannan shine karo na farko da kungiyar lafiya ta duniya da gwamnatin Koriya ke shirya irin wannan taro.

Kara karanta wannan

Karin Bayan: Manhajar WhatsApp Ta Dawo Aiki Bayan Daina Aiki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Lahadi, 23 ga watan Oktoba ne dai jirgin shugaban kasar ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke babbar birnin tarayya Auja zuwa kasar ta Koriya.

Ga wallafar tasa da hotunan taron a kasa:

2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bukaci yan Najeriya da kada su yi danasani kan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu ya ce kada su bari masu adawa su yaudare su cewa shugaban kasar bai tabuka komai ba tsawon shekaru bakwai da ya yi kan karagar mulki.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya yi jawabi ne a Kano yayin kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Dubai Ta Fitittiki Yan Najeriya 542 Daga Kasarta, Gwamnatin Najeriya ta kwaso su

Hadimin Buhari Ya Caccaki Peter Obi Kan Kaiwa Dubban Jama’a Tallafin Sunki 24 na Biredi

A gefe guda, Bashir Ahmad, mai bai wa shugaban kasan shawara kan sadarwa mai dogaro da fasahar zamani, ya zolayi Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar LP, kan tallafin da ya bai wa wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa dasu a jihar Anambra a baya-bayan nan.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, Obi ya bayyana wasu kayayyaki da ya bai wa mazauna yankin Ogbaru dake jihar Anambra da ‘yan gudun hijira a sansanin Atani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel