Za a Sheka Ruwa Yau Laraba, NiMet Ta Hango Matsala a Kano da Wasu Jihohin Arewa
- Hukumar NiMet ta yi hasashen hazo da hadari a sassa daban-daban na Najeriya a yau Laraba, tare da yiwuwar samun ruwan sama da tsawa
- Arewa za ta fuskanci yanayi mai zafi da matsakaicin ruwa, yayin da kudu za ta fuskanci ruwan sama mai ƙarfi da ka iya haifar da ambaliya
- Hukumar NiMet ta gargaɗi direbobi da matuƙan jirgin sama yayin da ta hango matsalolin da ka iya jawo asarar rayuka da dukiyoyi a yau Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Hukumar kula da yanayin sama ta ƙasa (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na yau Laraba, 29 ga watan Afrilu, 2026, inda ta bayyana cewa za a samu yanayi mabanbanta a faɗin ƙasar.
Yayin da sassan Arewa maso Gabas, da maso Yamma za su fuskanci yanayin zafi da ƙura, Arewa ta Tsakiya da Kudancin ƙasar za su samu ruwan sama da tsawa a yammacin yau.

Source: Original
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NiMet ta fitar a shafinta na X a yammacin ranar Talata, 28 ga Afrilu, 2026.
Hasashen yanayi a shiyyoyin Najeriya
Arewa ta Gabas da ta Yamma
A safiyar yau, ana sa ran rana za ta take, har ta yi zafi tare da ƙura a jihohin Borno, Yobe, Kano, Katsina, Bauchi da Jigawa.
Sai dai idan yamma ta yi, ana sa ran samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi da tsawa a jihohin Kaduna da Taraba.
NiMet ta yi gargadin cewa ƙurar da za a samu na iya rage gani ga masu ababen hawa, sannan za ta iya lalata kayayyakin da aka ajiye a waje.
Arewa ta Tsakiya
A Arewa ta Tsakiya kuwa, gami da birnin tarayya Abuja, za a samu haduwar hadari da safe. Idan rana ta ɗauki zafi zuwa yamma, za a samu ruwan sama da tsawa a Abuja da jihohin Kwara, Nasarawa, Kogi, Niger da kuma Plateau.
NiMet ta ce idan iskar ruwa ta fara kadawa, to za ta iya haddasa karyewar bishiyoyi da zasu iya jikkata mutane, da kuma lalata wasu kayayyaki da aka ajiye a waje.
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
Kudancin Najeriya zai fuskanci haduwar hadari a safiyar yau tare da yiwuwar yayyafi a Akwa Ibom da Cross River.
Amma daga yamma zuwa dare, za a samu gagarumin ruwan sama da tsawa a jihohi kamar su Ondo, Oyo, Osun, Edo, Imo, Abia, Enugu, Anambra, Bayelsa, da Rivers.
NiMet ta yi gargadin cewa mamakon ruwan da za a yi zai iya haifar da ambaliya a wasu wuraren, sannan guguwa mai ƙarfi na iya rage gani, ya jawo hadurra.

Source: Twitter
Muhimman shawarwari ga jama'a
Hukumar NiMet ta fitar da gargaɗi na musamman domin kiyaye rayuka da dukiyoyi:
- Ruwan tsawa na iya zuwa da guguwa; ku tabbatar kun adana abubuwan da iska za ta iya dauka.
- Direbobi su rage gudu yayin da ake ruwa saboda hanyoyi za su yi santsi sannan gani zai yi wahala sakamakon ƙura ko ruwan.
- A nemi mafaka a cikin gine-gine masu ƙarfi yayin da ake tsawa domin kauce wa fadawar walƙiya.
- Ana buƙaci kamfanonin jirage su riƙa samun bayanai daga NiMet na filayen jirgi kafin tashi ko sauka.
Karanta sanarwar NiMet a nan kasa:
Manyan Arewa sun magantu kan ambaliya
A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta nemi gwamnatoci da mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliya da su dauki matakan kariya.
ACF ta nuna damuwa kan hasashen da hukumar NIHSA ta fitar, wacce ta ce akalla garuruwa 1,249 a kananan hukumomi 176 na jihohi 30 da Abuja na fuskantar barazanar ambaliya.
Kungiyar ta bukaci hukumomin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su kara himma wajen wayar da kai da shirye-shiryen kariya game da ambaliya a Arewacin kasar.
Asali: Legit.ng


