Karo Na Uku a Jere, Shettima Ya Wakilci Tinubu a Wani Taro Da Aka Shiryawa Yan Takarar Shugaban Kasa

Karo Na Uku a Jere, Shettima Ya Wakilci Tinubu a Wani Taro Da Aka Shiryawa Yan Takarar Shugaban Kasa

  • Wata kungiyar mata ta shiryawa dukkanin masu neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 taro na musamman
  • Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya samu wakilcin abokin takararsa, Kashim Shettima a taron
  • Sauran yan takarar shugaban kasa da suka hada da Peter Obi, Hamza Almustapha da sauransu duk sun hallara a taron

Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya sake wakiltan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a wajen taron da aka shiryawa masu neman darewa kujerar Buhari gabannin zaben 2023.

Shettima ya hallara a wajen taron da gidauniyar Voice of Woman Empowerment Foundation tare da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur Foundation suka shirya.

Daily Trust ta rahoto cewa an yi taron ne a cibiyar taro na rundunar sojin sama da ke Abuja a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan PDP 5 Da Sukayi Watsi Da Atiku Suka Koma Bayan Peter Obi

Shettima da Tinubu
Karo Na 3 a Jere, Shettima Ya Wakilci Tinubu a Wani Sabon Taro Da Aka Shiryawa Yan Takarar Shugaban Kasa Hoto: APC Vanguard
Asali: Twitter

Sauran yan takarar shugaban kasa da suka hada da Peter Obi na Labour Party (LP), Prince Asewole Adebayo na Social Democratic Party (SDP) duk sun hallara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulmalik Ado Ibrahim ba Young Progressives Party (YPP), da Hamza Al-Mustapha na jam’iyyar Action Alliance (AA) suma sun halarci taron.

Tarukan da Shettima ya wakilci Tinubu

Wannan ba shine karo na farko da Shettima ke wakiltan Tinubu a wajen taron da aka shiryawa yan takarar shugaban kasa ba.

A watan Agusta, Shettima ya tsayawa Tinubu a taron NBA wanda aka yi a Eko Hotels, Victoria Island, a jihar Lagas.

Hakazalika, a watan Satumba, Shettima ya wakilci Tinubu a taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa.

Rashin ganin Tinubu wanda ya kai ziyarar aiki Kano ya haifar da damuwa game da lafiyarsa da kuzarinsa wajen neman takarar kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jiga-Jigan 'Yan PDP Da Suka Yi Watsi Da Atiku Suka Rungumi Obi

Sai dai a wajen ganawar da yayi da yan kasuwa a Kano a ranar Asabar, Tinubu ya yi watsi da rade-radin rashin lafiyarsa.

Shaidanun APC Sun Dade Da Komawa PDP, In ji Tsohon Minista

A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa shaidanun da ke cikin jam’iyyar APC duk sun koma PDP tun bayan da ya dawo jam’iyyar mai mulki a watan Satumban 2021.

Fani-Kayode wanda ya kasance mamba a kwamitin yakin neman zaben shugabancin Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV.

Ya jadadda cewa sam APCn da dana yanzu ba daya bane akwai bambanci sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel