Bayan Sauya Sheka, Tsohon Sakataren Katsina Ya Bukaci Mutane Su San Yan Takarar da Zasu Zaba a 2023

Bayan Sauya Sheka, Tsohon Sakataren Katsina Ya Bukaci Mutane Su San Yan Takarar da Zasu Zaba a 2023

  • Mustapha Inuwa ya gargadi gwamnatin jihar Katsina da manyan jami'anta kan takewa ma'aikata hakkinsu game da yan takarar da suke yi a 2023
  • Tsohon sakataren gwamnatin na Katsina ya shawarci masu zabe da su yi aiki da hankali yayin zaben wadanda suke so su shugabancesu
  • Inuwa ya nuna karfin gwiwar cewa PDP za ta kawo karshen gwamnatin APC duba ga abuuwan da ke faruwa a yanzu

Katsina - Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Dr. Mustapha Inuwa, ya gargadi gwamnatin jihar da manyan jami’anta da su daina takewa ma’aikata yancinsu na zaba ko hulda da yan takarar a suke muradi a zabe mai zuwa.

Inuwa ya kuma yi kira ga masu zabe da su kada kuri’unsu cikin hikima, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Mustapha Inuwa
Bayan Sauya Sheka, Tsohon Sakataren Katsina Ya Bukaci Mutane Su San Yan Takarar da Zasu Zaba a 2023 Hoto: Mallam Abdul Danja
Asali: Facebook

Tsohon SSG din ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Lahadi, a mahaifarsa ta Danmusa inda ya yanki tikitin kasancewarsa dan PDP, mako guda bayan ya sanar da ficewarsa daga APC tare da magoya bayansa.

Ya bukaci jama’a da su zabi PDP domin fita daga kangin rayuwa da suke ciki a yanzu, yana mai fada masu cewa kada su ji tsoron duk barazanar da wani zai yi masu a zaben 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yarda cewa da abubuwan da ke faruwa a bangaren siyasa a jihar Kaduna da karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina suna nuni ga karshen gwamnatin APC a kasar gabannin 2023.

Sai dai kuma, Inuwa ya karfafawa masu zabe gwiwar cewa kada su ki karbar kudin yan siyasa ko dan takara a yayin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

Amma ya yi kira garesu da su zabi yan takarar da suka dace wadanda za su gina gobensu da na yaransu dama na al’ummar kasar gaba daya.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

“Wannan taro na da muhimmanci da dumbin tarihi a jihar Katsina dama Najeriya baki daya.
“Ina mai godiya ga mutanen kirki na jihar Katsina, musamman na karamar hukumar Danmusa kan goyon baya da hadin kai da suke ci gaba da bani tun kafin yanzu.
“Ina mai rokon Allah ya ci gaba da taimaka mana a fafutuka da kokarin inganta rayuwar mutanen Katsina da ‘ya’yansu masu zuwa nan gaba.
“Ina mai kira gareku da yan Najeriya gaba daya da ku yi rijista da PDP da kara goyawa jam’iyyar baya don nasara a zaben 2023 mai zuwa.”

Tsohon Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

A baya Legit.ng ta kawo cewa tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina karkashin gwanna Amiju Bello Masari mai ci, Dr Mistapha Muhammad Inuwa ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Party zuwa Peoples Democratic Party, PDP.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Dan siyasar ya kuma kasance tsohon kwamishinan ilimi a jihar.

Inuwa wanda shine sakataren gwamnati mafi dadewa a jihar ya sanar da sauya shekarsa a ofishin kamfen dinsa a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel