Abdullahi Abubakar
7231 articles published since 28 Afi 2023
7231 articles published since 28 Afi 2023
Isra’ilawa daga bangarorin siyasa daban-daban sun nuna fushi kan yarjejeniyar farko tsakanin Amurka da Iran, suna kallonta a matsayin barazana ga tsaron Isra’ila.
Ƙasar Iran ta ce babu amfani da ci gaba da tattaunawar sulhu da Amurka bayan harin Isra'ila a Beirut, tana zargin Washington da kasa cika alkawuranta.
Sarkin Musulmi ya umarci daukacin Musulman Najeriya su fito domin neman ganin jinjirin watan Muharram 1448AH a ranar Litinin, 15 ga Yuni, bayan faduwar rana.
Hadimin gwamnan Benue kan harkokin matasa da yaɗa labarai, Atu Terver Joseph, ya yi murabus nan take saboda zargin rashin biyansa albashi tsawon watanni.
Wasu 'yan bindiga sun kutsa kauyen Ode Oriya da ke Owo a jihar Ondo, inda suka sace Baalen garin, Adeniyi Adelana, da dare tare da bindige matarsa yayin harin.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Fulani mazauna Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma sun fara barin yankunan saboda tsangwama da zargin aikata laifuka.
Ministan Tsaro a Najeriya, Christopher Musa, ya ce yaƙe-yaƙen Isra'ila da Iran da kuma na Rasha da Ukraine sun janyo ƙarancin kayan yaƙi a duniya.
Jam'iyyar ADC ta ki tabbatar da rahotannin da ke cewa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zabi Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakinsa.
Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa mutuwar Janar Sani Abacha ta bar masa shakku, yana mai cewa akwai abubuwan da suka nuna akwai wata makarkashiya.
Abdullahi Abubakar
Samu kari