'Babban Kuskure da Ƴan Najeriya Za Su Yi idan Suka Gujewa Zaɓen Tinubu a 2027'

'Babban Kuskure da Ƴan Najeriya Za Su Yi idan Suka Gujewa Zaɓen Tinubu a 2027'

  • Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce rashin sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027 zai zama babban kuskure ga ’yan Najeriya
  • Ya bukaci ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement ta yi kamfen bisa hujjoji da ƙididdigar ayyukan gwamnatin Tinubu tun bayan hawanta mulki a 2023
  • Ƙungiyar, wadda Tompolo ke jagoranta, ta ce tana son tattara aƙalla kuri’u miliyan 10 domin tabbatar da nasarar Tinubu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya yi magana game da zaben Bola Tinubu a 2027.

Kakakin Majalisar ya gargadi ’yan Najeriya cewa zaɓen wani ɗan takara a 2027 na iya zama babban kuskure.

Tajudeen Abbas ya shawarci yan Najeriya kan zaɓen Tinubu
Kakakin majalisar dokoki, Rt. Hon. Tajudeen Abbas. Hoto: House of Representatives.
Source: Twitter

Tajudeen ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba, yayin da yake jawabi ga tawagar PBAT Door-to-Door Movement da ta kai masa ziyara, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun jajubo rigima da jam'iyyar, an ba su wa'adi su gyara alaka da ita

Tajudeen Abbas ya yaba salon mulkin Tinubu

Ya ce zai zama rashin adalci idan ’yan Najeriya suka jure tsare-tsare da manufofin gwamnatin Tinubu, sannan su zaɓi wani shugaban da zai soke su.

Ya bukaci ƙungiyar ta gudanar da kamfen domin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu bisa la’akari da ƙididdigar ayyukan gwamnatin yanzu.

Ya ce zai kasance mai sauƙi a gabatar da ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ga ’yan Najeriya tare da samun sama da kuri’u miliyan 10.

Tajudeen ya bayyana cewa kamfen ɗin sake zaɓen Tinubu zai fi karkata ne kan hujjoji da ƙididdiga da ke nuna irin ci gaban da gwamnati ta samu tun 2023.

Tajudeen ya ce:

“Wannan kamfen ya kamata ya kasance bisa hujjoji da ƙididdiga. A bar mutane su ga kuma su ji irin abubuwan da gwamnati ta cimma cikin shekaru ukun da suka gabata.
“Kuma ba zai kasance abu mai wahala ba, domin duk mun san abin da wannan gwamnati ta yi a jihohi 36 na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yayyafa ruwan sanyi bayan kalaman Jingir sun ta da kura

“Saboda haka, kamfen ɗin zai kasance bisa hikima, balaga, hujjoji da ƙididdiga. Matukar kuka tsaya kan waɗannan abubuwa biyar, ba za ku yi kuskure ba.”
An fadi alherin Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Kokarin da Tinubu ya yi a Najeriya

Shugaban Majalisar Wakilan ya ce babu wata hukuma a matakin tarayya da ta fi Majalisar Wakilai kusanci da talakawa.

Ya ce majalisar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin ci gaba da mulkin gwamnatin Tinubu, cewar Daily Post.

Tajudeen ya ce:

"Ina tabbatar muku cewa za mu ci gaba da kasancewa cikin jakadun da za su wayar da kan jama’a game da hikimar ci gaba da mulki.
“Domin a ƙasar da aka yi shekaru sama da 40 cikin shekaru 60 na tarihinta ana tafiyar da ita ba daidai ba, babu shugaban da zai iya gyara duk kura-kuran baya cikin shekaru huɗu.
“Saboda haka, zai zama babban kuskure idan ’yan Najeriya suka mayar da baya kan ƙananan nasarorin da aka samu daga 2023 zuwa yanzu."

Za a kai tallan Tinubu Kano

Mun ji cewa wani kwamitin tallafa wa mazauna Kano ya shirya ƙaddamar da shirin ƙarfafa tattalin arziki domin samun goyon bayan Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Matawalle ya fito fili ya bayyana irin zaben da za a yi karkashin gwamnatin Tinubu

Shirin da Leke Abejide ke jagoranta zai tallafa wa matasa, mata, ’yan kasuwa, masu sana’o’i da ƙananan ’yan kasuwa a faɗin Kano.

Kwamitin ya ce shirin ba siyasa kawai yake nufi ba, zai samar da damarmaki, ƙarfafa al’umma da kuma ƙara shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.