Makinde Ya Yi Tunani, Ya Ɗauki Tsohon Daraktan DSS daga Katsina Mataimakinsa
- Dan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya zaɓi mataimakinsa wanda zai taya shi takara a zaɓen shekarar 2027
- Makinde ya zaɓi dan jihar Katsina a matsayin abokin takararsa yayin babban taron jam’iyyar APM da aka gudanar a Bauchi
- Gwamnan ya ce ya shirya fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga talauci, tare da magance matsalolin tsaro da inganta rayuwar jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Dan takarar shugaban kasa karkashin APM, Seyi Makinde ya zaɓi wanda zai taya shi takara a zaben 2027.
Makinde ya ɗauki tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, Lawal Musa Daura, a matsayin abokin takararsa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Oyo, Prince Dotun Oyelade, ya fitar, wanda Punch ta samu.
Ya ce Makinde ya yi zaɓin ne da gangan saboda ƙwarewar Daura wajen harkokin tsaro da leƙen asiri.
An bayyana Daura a matsayin abokin takarar Makinde yayin babban taron ƙasa na APM da aka gudanar a Rilwan Adamu Square da ke Bauchi.
Makinde ya ce ya zaɓe shi ne domin taimakawa wajen magance matsalolin tsaron ƙasar nan.
Sanarwar ta ce:
“Abokin takararsa na shugaban ƙasa shi ne Alhaji Lawal Musa Daura, tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta DSS daga shekarar 2015 zuwa 2018, wanda ya ce an zaɓe shi da gangan domin magance matsalar tsaron ƙasar nan.”
Daura ya jagoranci Hukumar SSS daga shekarar 2015 zuwa 2018, kafin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya cire shi daga mukaminsa
Makinde, wanda aka zaɓe shi a hukumance a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APM yayin taron, ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da ’yan siyasar da suke da irin hangen nesansa domin inganta Najeriya
Ya ce zai yi aiki tare da masu irin wannan manufa domin tabbatar da samun Najeriya mafi kyau nan da shekarar 2027
Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana da shirin fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga talauci, yana mai zargin cewa wasu manufofin da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata sun ƙara tsananta halin da ake ciki
Oyelade ya ce Makinde ya bayyana cewa yana da cikakken shiri na fitar da miliyoyin ’yan Najeriya daga talauci, wanda ya ƙara yin muni cikin shekaru uku da suka gabata sakamakon manufofin da ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba
Makinde ya kuma ce zaɓen Bauchi a matsayin wurin gudanar da taron yana da muhimmanci, saboda Bauchi ita ce mahaifar Firaministan Najeriya na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa
Fitowar Makinde a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APM da kuma zaɓar Daura a matsayin abokin takararsa na zuwa ne yayin da ake shirin babban zaɓen shekarar 2027
Yadda Makinde ya samu takara a APM
A baya, an ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya samu nasarar zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM a babban zaɓen 2027.
Shugaban APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ya miƙa masa takardar shaidar cin zaɓe da tutar jam’iyya a wani taro da ya gudana .
Dantalle ya ce nasarar Gwamna Makinde ta nuna fara wani sabon yunƙuri na sake gina Najeriya da haɗin kan masu neman sauyi.
Asali: Legit.ng

